An samu bullar wata mugunyar cuta mai yaduwa a China (Hotuna)

An samu bullar wata mugunyar cuta mai yaduwa a China (Hotuna)

Gwamnatin kasar China ta ce ta tabbatar da bullar wata cuta mai saurin yaduwa mai suna 'bubonic plague' wato annobar bubunic.

Hakan na zuwa ne watanni bayan bullar annobar COVID-19 da aka gano a birnin Wuhan a kasar ta China.

A cewar kafar watsa labarai na Xinhua, an samu mutum daya mai cutar a yankin Mongolia kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Hukumar Lafiya ta kasar ta ce an gano cutar a jikin wani makiyayi ne a ranar Lahadi amma baya cikin hatsari kuma ana masa magani a wani asibiti kamar yadda New York Times ta ruwaito.

An samu bullar wata mugunyar cuta mai yaduwa a China
An samu bullar wata mugunyar cuta mai yaduwa a China. Hoto daga The Cable
Asali: UGC

DUBA WANNAN: An kama matar kwamandan Boko Haram (Hoto)

CNN ta kuma ruwaito cewa an garzaya da wani yaro mai shekara 15 mazaunin Ulaankhus soum zuwa wani asibiti a ranar Lahadi bayan ya ci wata dabba mai kama da bera da kare ya farauto.

Hukumomi a kasar ta China sun yi gargadin mazauna kasar su dena farauta, ci ko safarar dabbobin da ka iya yada cututtuka kuma su kai rahoton duk wani dabba da suka ga ta mutu.

An samu bullar wata mugunyar cuta mai yaduwa a China
An samu bullar wata mugunyar cuta mai yaduwa a China. Hoto daga The Cable
Asali: UGC

Wannan gargadin na hana cin dabobin zai cigaba da aiki har zuwa karshen shekarar 2020 a cewar mahukunta kasar.

"A halin yanzu, akwai hatsarin yaduwar annobar a wannan garin. Ya kamata mutane su cigaba da kulawa da lafiyarsu su kuma kai rahoton duk wani ciwo da ba su gane kansa ba," kamar yadda China Daily ta ruwaito.

Micheal Head, babban mai binciken lafiya a Jamiar Southampton ya tabbatarwa CNN cewa bullar cutar "abin damuwa ne ga mutanen da ke zama a yankin na cikin Mongolia".

Ya kuma kara da cewa "ba za ta zama barazana ga duniya ba kamar yadda Covid-19 ta zama."

Wannan cutar tsohuwar annoba cewa a duniya da ta yi shekaru daruruwa da ta kashe mutane da yawa a tarihi.

Sai dai, ana iya maganin ta da magungunan kashe kwayoyin hallita wato antibiotics.

Wata kwayar hallita mai suna Yersinia pestis da ke zama a cikin wasu dabobi ne musamman dangin bera da kwarkwatarsu ke janyo cutar.

Wasu daga cikin alamominta sun hada da zazzabi, masasara, tari da kumburin wasu sassan jiki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel