Jami'an tsaro sun damke mata biyu da suka birne jaririya da ranta a Kaduna
Wata mata mai shekaru 33 da yayarta a Kaduna sun shiga hannun jami'an tsaro bayan an kamasu suna birne jaririya da ranta.
Matar mai suna Hauwa, ta je an cire mata jaririya daga cikin ta amma da taimakon yayarta mai shekaru 35. Sun hada kai wurin haka kabari suka birneta da ranta.
Kamar yadda rahoton ya bayyana, 'yan uwan biyu sun je wani otal a Tudun Wada Kaduna, inda suka kama daki don aikata mummunan laifin.
A yayin da suke haka wurin birne jaririyar, wani ya hangesu. Bayan kammalawa, sun rufe wurin da dutse.
Ganau ba jiyau ba ne ya sanar da hukumar otal din inda suka koma wurin da suka birne jaririyar.
A yayin hukumar otal din da aka birne jaririyar suke hake wurin, sun ga jini a ramin. Lamarin da yasa suka kira 'yan sanda suka kama matan biyu.
Har yanzu dai babu bayani cikakke na yadda aka cire jinjirar.

Asali: Twitter
KU KARANTA: Yanzu-yanzu: PSC ta kori manyan 'yan sanda 10 daga aiki
A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan jihar Sokoto ta kama wani mutum mai suna Shuaibu Aliyu sakamakon zarginsa da ake da dirkawa yarinya mai shekaru 14 ciki tare da yadda jaririyar da ta haifa a daji.
Kwamishinan 'yan sandan jihar, CP Sani Kaoje ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai bayan kama masu laifi.
Ya ce an damke wanda ake zargin da laifin fyade da kuma yunkurin kisan kai.
Kaoje ya bayyana cewa, "wani Alhaji Hamisu Abubakar da ke yankin Kalambaina a karamar hukumar Wamakko ta jihar Sokoto ya kai korafi ofishin 'yan sanda.
"Ya ce wani mutum mai suna Shuaibu Aliyu ya ja yarinya mai shekaru 14 cikin dakinsa inda yayi mata fyade."
Ya kara da cewa, "Sakamakon hakan, ta samu ciki har ta haihu. Ta kai wa wanda ake zargin jinjirin tare da wani abokinsa Nasiru Attahiru wanda yanzu ake nema.
"Sun karba tare da jefar da jinjirin a wani daji da ke kauyen Gidan Boka a karamar hukumar Wamakko ta jihar Sokoto."
Kwamishinan 'yan sandan ya kara da cewa wani mutumin kirki ne ya tsinta jinjirin tare da sanar da 'yan sanda. Ya ce an damke wanda ake zargin kuma ya amsa laifinsa.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng