Zaben Gwamnan Ondo: PDP ta zabi Matawalle ya jagoranci kwamitin yakin neman zabe

Zaben Gwamnan Ondo: PDP ta zabi Matawalle ya jagoranci kwamitin yakin neman zabe

Kwamitin gudanarwa na jam'iyyar PDP na kasa, ya amince da nadin Gwamna Muhammadu Bello Matawalle na jihar Zamfara, a matsayin wanda zai jagoranci kwamitin yakin neman zaben gwamnan jihar Ondo.

Babban sakatare a kwamitin gudanarwa na jam'iyyar, Austin Akobundu, shi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin cikin birnin Abuja.

Mista Akobundu ya ce, kwamitin ya kuma amince da nadin Cynthia Egwa, David Vaughan da Ginger Onwusibe a matsayin mambobin kwamitin da Gwamna Matawalle zai jagoranta.

Kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito, kwamitin ya kuma amince da Kingsley Chinda a matsayin sakatare.

Gwamna Muhammad Bello Matawalle na jihar Zamfara
Gwamna Muhammad Bello Matawalle na jihar Zamfara
Asali: Twitter

Ya ce an ratayawa kwamitin nauyin zaben wakilan zabe uku a kowane daya daga cikin mazabu 203 da ke fadin jihar.

An shirya fara wannan aiki ne a ranar Laraba, 8 ga watan Yuli a duk fadin jihar.

Tun tsawon watanni da suka gabata, hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta INEC, ta sanya ranar 10 ga watan Oktoba a matsayin ranar da za a gudanar da zaben gwamnan Ondo.

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, kwamitin gudanarwa na jam'iyyar PDP, a ranar Juma'ar da ta gabata, ya nada gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike a matsayin shugaban kwamitin yakin neman zaben gwamnan jihar Edo.

KARANTA KUMA: Gwamnatin Tarayya ta bai wa jihohi umarnin bude makarantu

Jam'iyyar ta sanar da hakan ne a kan shafinta na Twitter, inda ta bayyana gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, a matsayin mataimakin kwamitin yakin neman zaben.

Wannan lamari ya faru ne kwana daya bayan da jam'iyyar APC ta nada gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, a matsayin shugaban kwamitin yakin neman zaben gwamnan jihar ta Edo.

A ranar Asabar, 19 ga watan Satumba na 2020, za a gudanar da zaben gwamna a jihar Edo, inda gwamna mai ci Godwin Obaseki, zai gwabza da dan takara na jam'iyyar APC; Osagie Ize-Iyamu.

Makonni kadan da suka gabata ne Gwamna Godwin Obaseki dai ya sauya sheka daga APC ya koma PDP kuma jam'iyyar ta tsayar da shi takara ba tare da wata-wata ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel