Babu jihar da ta kai Kano samun yawan waraka daga cutar Korona

Babu jihar da ta kai Kano samun yawan waraka daga cutar Korona

Jihar Kano ta yi fintinkau wajen yawan adadin masu samun waraka daga cutar Coronavirus, bisa alkaluman hukumar hana yaduwar cutuutuka a Najeriya wato NCDC, Channels TV ta binciko.

Wata daya yanzu, a ranar Lahadi, 5 ga Yuni, 2020, jihar Kano na da mutane 1,264 masu cutar amma 1,024 sun samu waraka.

Hakan ya nuna cewa kimanin kashi 63% suka samu waraka a jihar, mafi yawa cikin dukkan jihohin Najeriya.

Duk da cewa a ranar Lahadi, jihar Legas ta samu adadin masu waraka mafi yawa a Najeriya - 1,653 - adadin masu cutar ya ninka hakan fiye da sau goma.

Rahoton NCDC ya nuna cewa cikin wadanda suka kamu da cutar a Kano, 52 suka mutu yayinda 188 ke jinya yanzu.

Babu jihar da ta kai Kano samun yawan waraka daga cutar Korona
Babu jihar da ta kai Kano samun yawan waraka daga cutar Korona
Asali: Facebook

KU KARANTA: Ba zamu kara baiwa masu fyade beli ba, muna shawarar fara dandankesu - El-Rufa'i

Za ku tuna cewa a ranar 11 ga watan Afrilu jihar Kano ta samu bullar cutar Coronavirus, kwamishanan lafiyan jihar, Aminu Tsanyawa ya bayyana haka.

Bayan kimanin mako daya a ranar 16 ga Afrilu, jihar Kano ta samu mutuwar mutum na farko sakamakon cutar kuma adadin masu cutar yayi tashin gwauron zabo.

Hakazalika aka fara samun yawaitar mace-mace a jihar, masu hakar kabari a cikin birnin Kano suka shaida.

Sakamakon wannan mace-mace, gwamnatin tarayya ta tura kwamiti na musamman zuwa Kano don duba lamarin.

Yayinda ziyarar, ministan lafiya, Dakta Osagie Ehanire, ya ce da yiwuwa cutar COVID-19 ta sabbaba macen-macen da ake yi a Kano.

Rahoton kwamitin fadar shugaban kasa na yaki da cutar COVID-19 wato PTF ya nuna cewa Korona ce tayi sanadiyar mutuwar kashi 60% na mace-macen jihar.

Gwamnatin jihar Kano ta musanta wannan rahoto kuma tayi watsi da shi. Gwamna Abdullahi Ganduje ya ce duk karya ne.

Cikin kankanin lokaci jihar Kano ta samu cibiyoyin gwajin cutar guda biyar, fiye da kowace jihar a Najeriya face Legas.

Bayan makonni, a ranar Alhamis da ta gabata gwamna Ganduje ya dakatad da dokar kullen data sanya a jihar.

Ya haramta talla, da bara kuma ya wajabta sanya takunkumin fuska a bainar jama'a.

Hakazalika gwamnan ya sanar da cewa yan makaranta dake ajin karshe zasu iya komawa yayinda ya umurci ma'aikata daga Lvl 12 su koma bakin aiki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel