Sabbin mutum 575 sun kamu da cutar korona a Najeriya

Sabbin mutum 575 sun kamu da cutar korona a Najeriya

Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa a Kasa (NCDC) ta ce annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 575 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NCDC ta fitar da misalin karfe 11.43 na daren ranar Litinin 6 ga Yulin shekarar 2020.

A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa karin sabbin mutum 575 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka;

Sabbin mutum 575 sun kamu da cutar korona a Najeriya
Sabbin mutum 575 sun kamu da cutar korona a Najeriya
Asali: Twitter

Lagos-123

FCT-100

Delta-58

Edo-52

Ogun-42

Katsina-24

KU KARANTA: An kama matar kwamandan Boko Haram da ɗan leƙen asiri

Bayelsa-23

Rivers-22

Borno-19

Plateau-18

Ondo-18

Oyo-17

Kwara-15

Osun-13

Enugu-9

Nasarawa-7

Abia-6

Cross River-5

Kaduna-3

Ekiti-1

Alkalluman da hukumar ta dakile cututtukan ta fitar a ranar Litinin 28 ga Yunin shekarar 2020 ya nuna cewa jimillar wadanda suka kamu da cutar ta korona a kasar 29,286.

An sallami mutum 11,828 bayan an tabbatar da sun warke sarai, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 654.

A wani labarin daban, kun ji cewa Eunice Ortom, matar gwamnan jihar Benue, ta kamu da kwayar cutar COVID-19 da aka fi sani da coronavirus kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Matar gwamnan da fitar da sanarwar hakan a daren ranar Juma'a inda ta ce dan ta da wasu maaikatanta suma sun kamu da cutar.

Ta shawarci dukkan wadanda suka gana da ita a baya bayan nan su killace kansu kuma su tafi ayi musu gwajin na COVID-19.

Eunice ta ce kamuwa da cutar baya nufin mutum zai mutu tare da cewa tana fitar dan ta da ita za su warke.

"A daren yau, na samu sakamakon gwajin da hukumar NCDC ta yi min a kamar yadda aka saba yi a gidan gwamnati a Makurdi kuma sakamakon ya nuna ni da da na da wasu maaikata na mun kamu," a cewar sanarwar.

"A halin yanzu mun killace kan mu kamar yadda kaidar cutar ta ke kuma za mu fara shan magunguna a karkashin kulawar likitoci.

"Duk da cewa na kira dukkan wadanda na san na yi cudanya da su na fada musu su tafi gwaji, ina shawartar duk wanda ya yi cudanya da ni cikin makonni biyu da suka gabata ya tafi a gwada shi.

"Ina son tunatar da mutane cewa COVID-19 ba ya nufin mutuwa duba da adadin mutanen da ke warkewa kawo yanzu saboda haka kowa ya kwantar da hankalinsa amma akwai bukatar mu cigaba da kulawa.

"Ina shawartar mutane su cigaba da kiyaye kansu da bin dokokin hukumomin lafiya. Ku kasance lafiya! COVID-19 gaskiya ne!."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel