An kama matar kwamandan Boko Haram (Hoto)

An kama matar kwamandan Boko Haram (Hoto)

Rundunar Sojin Najeriya ta ce ta kama matan wani kwamandan Boko Haram da wani ɗan leƙen asiri.

An kuma kama wasu ƴan ta'adda hudu da matan ɗan leƙen asiri, Aishatu Manye da Kelune Mate a Gajingi da ke ƙaramar hukumar Madagali na jihar Adamawa.

Shugaban sashin watsa labarai na sojojin Najeriya, John Enenche ne ya sanar da hakan.

An kama ɗan leƙen asirin Boko Haram yayin sallar Juma'a a Michika a Adamawa kamar yadda The Nation ta ruwaito.

An kuma kama wani mayaƙin Boko Haram bayan arangama da aka yi a Miyanti a ƙaramar hukumar Bama na jihar Borno.

An kama matar kwamandan Boko Haram da ɗan leƙen asiri
An kama matar kwamandan Boko Haram da ɗan leƙen asiri. Hoto daga The Nation
Asali: UGC

KU KARANTA: Na kama matata a ƙarƙashin gadon kwartonta tsirara - Miji ya faɗa wa kotu

Har wa yau, wasu ƴan ta'adda uku; Mohammed Babagana, Modu Jugudun da Alhaji Usman sun miƙa kansu ga sojojin Delta Company da ke Pulka a ƙaramar hukumar Gwoza.

Kazalika, wani Mustapha Kori ya mika kansa ga sojojin da ke sansanin Camp 11 da ke Gamboru a ƙaramar hukumar Ngala a Borno.

Sanarwar ta ƙara da cewa a watan Yuni, dakarun sojojin sun ceto farar hula 35 daga hannun ƴan ta'addan Boko Haram/ISWAP.

Sun haɗa da mata 18, yara 16 da wani babban mutum ɗaya.

"Ba tare da ɓata lokaci ba an baiwa yaran rigakafin cutar shan inna yayin da su kuma matan aka ba su taimakon farko," in ji Enenche.

A wani labarin daban, kun ji cewa wata majiya daga rundunar sojojin Najeriya ta ce Boko Haram suna samun makamai da motocci ne yayin harin da suke kai wa sansanin sojoji a yankin Arewa maso Gabas.

Rundunar ta bayyana hakan ne yayin mayar da martani a kan ikirarin da kakakin rundunar tsaro, Manjo Janar John Enenche ya yi na cewa rundunar soji ba ta san wadanda ke daukan nauyin 'yan ta'adda ba da inda suke samo makamai.

"Ba gaskiya bane a ce makaman da 'yan ta'addan ke amfani da shi yana da banbanci da wadanda muka siyo," a cewar daya daga cikin majiyar.

"Maganar gaskiya shine mafi yawancin motocin, tankunan yaki da sauran makamansu daga sansanin mu suka sace. Idan kana iya tunawa, su kan sace makamai daga sansanin mu da suka kai hari. Yawancin motocin da suke amfani da shi daga wurin dakarun mu suka sace.

"Kuma suna samun makamai daga kasashen da muke makwabtaka da su na kusa da yankin tafkin Chadi a farashi mai rahusa. Safarar makamai daga yankin Tafkin Chadi yana da sauki saboda rashin tsaro a iyakoki," in ji majiyar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel