Yanzu-yanzu: An gayyaci Ibrahim Magu, shugaban EFCC amsa tambayoyi

Yanzu-yanzu: An gayyaci Ibrahim Magu, shugaban EFCC amsa tambayoyi

An gayyaci mukaddashin shugaban hukumar yaki da rashawa da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, (EFCC) gaban kwamiti don bayani a kan ayyukan hukumar.

An gano cewa, kwamitin na wannan zaman ne a 'Banquet Hall' da ke fadar shugaban kasa.

An tsare Magu a cunkoson motoci da ke wucewa zuwa anguwar Wuse II na EFCC a Abuja kuma aka mika masa goron wannan gayyatar.

Duk da Magu na kan hanyarsa ta zuwa hedkwata, ya roki jami'in da ya tsaresa a kan ya bar sa inda daga baya sai ya amsa wannan gayyatar.

Amma kuma an sanar da shi cewa gayyatar wannan kwamitin ta fi muhimmanci.

Wurin karfe 1:35 na rana, Ibrahim Magu ya isa fadar shugaban kasa inda aka shigar da shi inda zai yi bayanan.

A wannan lokacin, lauyan Magu, Rotimi Oyedepo, ya samesa a fadar shugaban kasar.

Wata majiya ta ce: "Magu da Jacob a halin yanzu suna wani ofishin da ke fadar shugaban kasar.

"Ba a kama shi ba, kuma babu wata hukumar tsaro da ta damke shi. Muna sauraron ci gaban da zai faru a gaba."

Karin bayani na nan tafe...

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel