Waiwaye: Gwamnatin Yar’Adua ta gaza - Buhari, Atiku da sauransu

Waiwaye: Gwamnatin Yar’Adua ta gaza - Buhari, Atiku da sauransu

A yayin da tsohon shugaban Najeriya, Marigayi Umaru Yar'Adua ke kan ganiyar mulki a kasar, an samu 'yan siyasa da dama da suka yi wa gwamnatinsa ta jam'iyyar PDP adawa.

Shugaba Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC, na daya daga cikin jiga-jigan 'yan siyasa da suka yi wa gwamnatin marigayi adawa, inda har ya misalta gwamnatinsa a matsayin wadda ta gaza.

Tarihi ya nuna cewa, an yi wa Marigayi Yar'adua adawa a yayin da aka fara yada jita-jita a kan cewa zai sake tsayawa takarar shugabancin kasar bayan ya kammala wa'adinsa na farko.

Wannan lamari ya sanya aka gudanar da wani taron jiga-jigan 'yan siyasa da tsaffin masu rike da madafan iko na kasar a watan Oktoban shekarar 2019.

Shugaba Buhari; tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar da kuma tsohon gwamnan jihar Sakkwato, Alhaji Attahiru Bafarawa, su ne suka kira wannan babban taro.

Sai dai wasu daga cikin fusatattun jam'iyyar PDP da aka yi tsammanin ganinsu a taron ba su halarce shi ba, amma hadimai da abokan huldar kusoshin jam'iyyar sun samu damar zuwa.

Marigayi Tsohon Shugaban kasa Umaru Yar'Adua
Marigayi Tsohon Shugaban kasa Umaru Yar'Adua
Asali: UGC

Yayin gabatar da jawabai a taron na sirrance, Atiku ya nemi 'yan Najeriya da su yi watsi da jam'iyyar PDP yayin da ta kudirci mayar da kasar kan tsarin siyasa na jam'iyya daya tilo.

Wadanda suka halarci taron sun hada da tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Cif Olu Falae; tsohon Ministan Yada Labarai, Cif Dapo Sarumi, da tsohon Ministan Harkokin Waje, Cif Tom Ikimi.

KARANTA KUMA: Zaben Edo: Ganduje da Buni sun isa ofishin APC domin karbar rantsuwa

Sauran sun hada da Tsohon karamin Ministan Harkokin Waje, Cif Dubem Onyia; Tsohon Ministan Ilimi, Alhaji Dauda Birma; Tsaffin Gwamnoni Ashiek Jarma da Saidu Barda.

Haka kuma taron ya samu halarcin Tsohon Shugaba Mai Rinjaye a Majalisar Dattawa; Sanata Lawali Shu'aibu da kuma Tsohon Shugaban Marasa Rinjaye a Majalisar Dattawa; Sanata Daniel Saror.

Buhari, wanda ya jagoranci taron, ya ce: "A yau muna magana ne game da gwamnatin da ta gaza a mafi muhimmancin nauyin da ya rataya a wuyan gwamnati na kiyaye doka da oda da samar da ingantaccen yanayi."

"Wannan gwamnatin da wadda ta gabace ta sun kasa magance matsalar tsaro wacce ta kasance mai matukar tayar da hankali ta yadda babu wanda yake zaune lafiya a duk lokacin da yake gida, kan hanya ko ma a gado."

"A kullum ana ci gaba da karya doka a tsakanin al'umma a fadin tarayyar kasar."

Buhari ya ambaci rashin lafiyayyun tituna da tabarbarewar harkar ilimi a matsayin gazawar gwamnatin wajen sauke nauyin da rataya a wuyanta wanda a cewarsa ya samo asali ne tun daga tsohuwar gwamnatin Olusegun Obasanjo.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel