Yanzu-yanzu: Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ya warke daga Coronavirus

Yanzu-yanzu: Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ya warke daga Coronavirus

Bayan kwanaki 7 da killace kansa bayan kamuwa da cutar nan mai toshe numfashi watau Coronavirus, gwamnan jihar Ondo, Arakurin Rotimi Akeredolu, ya samu waraka daga cutar.

The Punch ta ruwaito cewa Gwamna Akeredolu ya bayyana hakan ne a hirarsa da manema labarai a ranar Litinin.

Yace Likitocinsa sun tabbatar masa da hakan bayan gwaji biyu da aka yi masa.

Akeredolu ne Gwamna na biyar da ya samu waraka cikin gwamnoni bakwai da suka kamu da cutar Korona.

Sauran da ke jinya har yanzu sune gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, da Gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi.

Yanzu-yanzu: Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ya warke daga Coronavirus
Yanzu-yanzu: Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu
Asali: Depositphotos

A ranar Talata, 2 ga watan Yuli, gwamnan jihar Ondo, ya sanar da cewa ya kamu da cutar COVID-19.

Amma Akeredolu ya bayyana cewa duk da cewa yana killace, ba zai mika ragamar mulki hannun mataimakinsa ba.

Gwamnan ya shiga takun tsaka da mataimakinsa tun gabanin zaben Shugaban kasa 2019.

Haka suka cigaba da zaman doya da manja har sai yanzu da mataimakin ya sauya sheka zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party PDP.

A lokacin da cutar Korona ta kama Gwamnan, mataimakin ya bukacesa ya mika masa ragamar mulki tunda yana kwance yanzu.

Gwamnan yace sam ba zai mika masa ba.

Daga baya mataimakin ya baiwa gwamnan wa’adin kwanaki 21 ya mika masa mulki ko su garzaya kotu.

Amma cikin kwanaki bakwai, Gwamnan ya samu lafiya.

Daga samun lafiyarsa kuma, Mista Idefayo Abegunde, sakataren gwamnatin jihar Ondo, ya yi murabus daga mukaminsa a yau, Litinin, 06 ga watan Yuli, 2020.

Sai dai, Abegunde ya yi gum da bakinsa a kan dalilin da yasa ya zabi yin murabus.

Shi kuma Gwamnan ba tare da bata lokaci ba ya maye gurbinsa da Taiwo Oluwatuyi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel