An yi gobara a gidan wuta a jihar Kano

An yi gobara a gidan wuta a jihar Kano

Mun samu rahoton cewa, a ranar Litinin, 6 ga watan Yuli, an yi gobara a gidan wutar lantarki na Kofar Dan-Agundi da ke kwaryar birnin Kanon Dabo.

Wannan tasha ita ce babbar jigo cikin hanyoyin rarraba wutar lantarki mallakar hukumar samar da wutar lantarki ga jihohin Kano, Katsina da kuma Jigawa (KEDCO).

Sashen Hausa na Jaridar Daily Trust ya ruwaito cewa, gobarar wadda ta tashi da misalin karfe 11.00 na safe, ta yi sanadiyar konewar daya daga cikin injinan rarraba wuta.

Sai dai rahotanni sun bayyana cewa, jami'an hukumar kwana-kwana na jihar, sun samu nasarar kashe wutar gabanin ta yi wannan mummunan ta'adi.

Kakakin hukumar kwana-kwana na jihar, Sa'idu Muhammad, shi ne ya bayar da tabbacin wannan rahoto kamar yadda jaridar Kano Today ta ruwaito.

Gidan Wuta na Kofar Dan Agundi yayin da gobarar ta ke ciki
Hakkin mallakar hoto; Jaridar Daily Trust
Gidan Wuta na Kofar Dan Agundi yayin da gobarar ta ke ciki Hakkin mallakar hoto; Jaridar Daily Trust
Asali: Twitter

Babu rai ko daya da ya salwanta yayin da gobarar ta tashi inji kakakin hukumar kwana-kwanan.

Sai dai ya kuma bayyana cewa, an tsunduma cikin bincike domin gano musabbabin wannan gobara.

"A yayin da gobarar ta tashi, ma'aikatan tashar sun kashe dukkan na'urorin wutar da ke gidan cikin gaggawa kafin daga bisani 'yan kwana-kwana su zo su kashe wutar", inji wani ganau a wajen da wutar ta kama.

KARANTA KUMA: Saudiyya ta haramtawa Mahajjata sanya hannu jikin Ka'aba a aikin Hajjin bana

A wani rahoto mai nasaba da wannan da jaridar Legit.ng ta ruwaito, kimanin mutane 16 ne suka rasa rayukansu a sanadiyar musibu na gobara daban-daban da suka auku cikin watan Yuni na shekarar da muke ciki a jihar Kano.

Kakakin hukumar kwana-kwana na jihar, Saidu Muhammed, wanda ya bayyana hakan a karshen makon da ya gabata, ya ce lamarin ya kuma janyo asarar kadarori da darajarsu ta kai naira miliyan 40.6 a cikin wannan lokaci.

Muhammed ya ce, a yayin gudanar da ayyukan agaji da kai dauki da suka rataya a wuyansu, sun samu nasarar ceto rayukan mutane 71 da dukiya wadda ta kai naira miliyan 120 a cikin bala'o'i na gobara 51.

A cewarsa, "Ma'aikatar ta kuma samu kiraye-kiraye na neman kawo dauki har sau hamsin, yayin da kuma aka yi musu kira na karya guda 9 daga mazauna gari."

"Ya alakanta aukuwar wannan bala'o'i na gobara da hatsarin mota, amfani da kayayyakin lantarki da makamashin gas ko fetur."

"Ya kuma shawarci mazauna jihar da su yi taka tsantsan yayin amfani da kayayyakin lantarki don kauce wa aukuwar gobara," inji Muhammed.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel