CBN ta sake rage wa Naira daraja

CBN ta sake rage wa Naira daraja

Babban bankin Najeriya a ranar Talata ya rage darajar Naira. Dala daya a halin yanzu na da darajar N381. Hakan na daga cikin hanyar gyara yanayin cinikayya tare da tabbatar da daidaituwa.

Duk da babban bankin bai fito ya sanar da matsayarsa ba, bayanin da aka samu daga adireshin yanar gizo na FMDQ OTC game da darajar naira, ya nuna sauyin kashi 5.54. Da farko dala daya tana daidai da N360 amma a halin yanzu ta koma N381.

Sabuwar darajar Nairar da babban bankin Najeriya ya fitar, ya biyo bayan kokarin bankin na mayar da yanayin cinikayya bai daya da na sauran kasashen ketare.

Ana tsammanin kudin shiga zai samu karuwa koda kadan ne ta fuskar tattalin arzikin Najeriya sakamakon rage darajar naira da aka yi, cewar wani mai kiyasi mai suna Omotola Abimbola, mazaunin jihar Legas.

CBN ta sake rage wa Naira daraja
CBN ta sake rage wa Naira daraja. Hoto daga Premium Times
Asali: UGC

KU KARANTA: Alkali ya daure ma'auratan da suka kafa wa 'yar aiki kusa a kai, konata da kuma saka mata makami a gaba

A wani labari na daban, Laolu Akande, kakakin mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce babu kamshin gaskiya a cikin wasu rahotanni da ke ikirarin cewa maigidansa ya karbi biliyan N4 daga hannun Ibrahim Magu.

Wasu kafafen yada labarai sun wallafa cewa Magu, dakataccen mukaddashin shugaban hukumar EFCC, ya sanar da kwamitin bincike cewa ya bawa mataimakin shugaban kasa biliyan N4 daga kudaden da aka kwace a hannun mabarnata.

A cewar rahotannin, Magu ya sanar da kwamitin cewa ya bawa Osinbajo kudin ne bayan ya nemi a sakar ma sa wani bangare na kudaden da EFCC ta kwace. Sai dai, a cikin wani jawabi da

Akande ya aikewa manema labarai ya bayyana wadancan rahotanni a matsayin na 'kanzon kurege' da babu gaskiya a cikinsu.

"Ya kamata mu sanar da jama'a cewa babu gaskiya a cikin rahotannin da ake yadawa, mu na da sahihan bayanai a hannunmu, kawai ana son kawo rudani ne ga kwamitin da ke binciken Ibrahim Magu.

"Mun san da cewa ana amfani da wasu kafafen yada labarai da ake biya domin cin mutunci ko bata sunan wasu mutane ko kuma don kawai a haifar da rudani a tsakanin jama'ar Najeriya," a cewar Akande.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel