An kashe mutum uku, an sace shugaban jam'iyyar APC a Katsina

An kashe mutum uku, an sace shugaban jam'iyyar APC a Katsina

Rayukan mutum uku sun salwanta a wani sabon hari da 'yan bindiga suka kai wasu kauyuka a karamar hukumar Matazu ta jihar Katsina.

Yayin harin na dare da 'yan bindigar suka kai a karshen makon da ya gabata, sun kuma yi awon gaba da shugaban jam'iyyar APC na karamar hukumar, Yusha'u Dissi tare da wata mata.

Haka zalika a wannan dare, 'yan bindigar sun kai hari wasu kauyuka na karamar hukumar Batsari ta jihar kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

A kauyen Dan Alhaji, 'yan bindiga sun bude wa mutanen kauyen wuta ta harsashin bidiga kan mai uwa da wabi, inda suka kashe mutum daya.

Gwamman jihar Katsina; Aminu Bello Masari
Hakkin mallakar hoto; Fadar gwamnatin Katsina
Gwamman jihar Katsina; Aminu Bello Masari Hakkin mallakar hoto; Fadar gwamnatin Katsina
Asali: Facebook

Maharan sun kuma yi lalube gida-gida a kauyen Kimbitsawa, inda a nan suka yi awon gaba da shanu guda 18.

Rahotanni sun bayyana cewa, maharan sun balle shagunan masu tireda da dama inda suka kwashi kayan abinci da sauran kayayyaki na masarufi.

A kauyen Kandawa, maharan sun kashe mutum guda yayin da da suka yi garkuwa da wasu mutum uku.

KARANTA KUMA: SERAP ta ba Buhari wa'adi ya nemo N300m da aka nema aka rasa a asusun gwamnati

Sai kuma kauyen Shirgi, an ruwaito cewa maharan sun kashe wani saurayi mai shekaru 12, yayin da kuma suka harbe mutane da dama a kauyen Tsugunni, inda a nan ma sun saci dabbobi fiye da 60.

A ranar Asabar da daddare cikin kauyen Wurma na karamar hukumar Kurfi ta jihar, an sace mata takwas wanda har yanzu babu wani amo ballantana labarinsu.

Yayin da manema labarai suka tuntubi iyalan Dissi a daren jiya, sun ce har kawo yanzu ba su da wata masaniya inda yake.

A wani rahoton kuma, Legit.ng ta ruwaito cewa, Alhaji Mahdi Shehu, fitaccen ‘dan kasuwa a Najeriya, ya shiga gidan rediyon Freedom da ke jihar Kaduna, inda ya jefi gwamnatin jihar Katsina da zargin batar da kudin tsaro.

Mahdi Shehu ya zargi gwamnatin Rt. Hon. Aminu Bello Masari ta yi ruf da cikin kan fiye da Naira biliyan 24 wanda aka warewa jihar domin magance matsalar tsaro.

Wannan Bawan Allah ya bayyana cewa gwamnatin Katsina ta wawuri Naira miliyan 500 daga cikin asusun tsaro, wanda ta ce ta batar wajen taron jam’iyyar APC na kasa a 2018.

Shararren ‘dan kasuwan ya bayyana cewa ya na da hujjoji da ke nuna yadda aka rika sama-da-fadi da kudin da ya kamata ace an yi amfani da su wajen tsare rai da dukiyar Katsinawa.

A cewar Shehu, gwamnatin mai girma Aminu Masari ta kashe fiye da Naira miliyan 500 da sunan sayen wayoyin salula ga masu mulki a jihar Katsina. Wadannan wayoyi sun tashi a kan kusan Naira miliyan takwas.

Haka zalika ana zargin gwamnatin APC mai-ci a Katsina da fitar da fiye da Naira miliyan 250 wajen daukar dawainiyar malaman addinin musulunci na kungiyar JIBWIS.

A binciken da wannan Attajiri ya ce ya yi, gwamnatin Katsina ta batar da sama da Nira miliyan 600 da sunan albashin masu gadin wurin aikin samar da lantarki da karfin iska a garin Rimi.

Da ya sake fitowa a wani karo a ranar Asabar, Mahdi Shehu ya zargi gwamnatin Katsina da kashe N40m da N21m wajen sayawa hukumar DSS manhaja da kuma gyaran jirgin sojin sama na kasa a 2017.

Tsakanin 2015 zuwa 2018, ‘dan kasuwan ya ce an yi gaba da N4.7b da sunan tallafi ga jami’an tsaro a jihar ta Katsina.

Haka kuma an batar da N1.3994b da nufin tallafawa shugaban bataliyar sojojin kasa da ke jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel