Allah mai iko: Yadda mata ta haihu bayan shekaru 10 da daukar ciki

Allah mai iko: Yadda mata ta haihu bayan shekaru 10 da daukar ciki

- Elizabeth Packal matashiya ce mai shekaru 23 daga kasar Togo amma tana zama a jihar Oyo

- Ta bayyana yadda ta haihu bayan daukar ciki tun tana da shekaru 13 a duniya

- Matashiyar da bata sanar da wanda yayi mata cikin ba, ta haihu a ranar 20 ga watan Maris na 2020

Wata matashiya mai shekaru 23 'yar asalin Togo mai suna Elizabeth Packal mai zama a Oyo ta haifa yarinya mace bayan shekaru 10 da daukar ciki.

Legit.ng ta ruwaito cewa, bayan haihuwar da Elizabeth tayi, bata san wanda yayi mata ciki ba saboda ciwon da ya rike cikin har na tsawon shekaru 10.

Elizabeth mai zama a kauyen Eiyeosoka da ke Ofiki a karamar hukumar Atisbo ta jihar Oyo, ta haihu a ranar 20 ga watan Maris wurin karfe 7:45 a asibitin Alaafia Tayo da ke titin Irawo-Owode.

Likitan da ya karba haihuwar, Dr Okawoyin David ya bayyana cewa lokacin da aka kawo Packal asibitin, ya tambaya wanda ya tabbatar da tana da ciki.

Mahaifinta, Ahmadu Guruma Packal, ya ce bai san yanayin ciwonta ba amma an kaita asibitoci daban-daban. Babu jimawa kuwa ta haifo yarinya mace.

Daga Guruma har Dr Olawoyin sun sha matukar mamaki bayan haihuwar Elizabeth, kuma mahaifinta ya tabbatar da cewa tun 2010 take fama da rashin lafiyar.

Dr Olawoyin ya ce akwai yuwuwar wani ciwo ne a jikinta kafin ta samu cikin don kuwa bayan haihuwar da tayi, cikinta ya kumbura kamar akwai wani cikin.

Olawoyin ya jaddada cewa akwai matukar wuya ciwo ya zauna tare da ciki. Akwai babban abun mamaki.

Amma kuma har a halin yanzu, ba a san wanda ya dirka wa Elizabeth ciki ba.

Allah mai iko: Yadda mata ta haihu bayan shekaru 10 da daukar cikin
Allah mai iko: Yadda mata ta haihu bayan shekaru 10 da daukar cikin
Asali: UGC

KU KARANTA: Boko Haram: Yadda sojin sama suka ragargaza sabbin shugabannin 'yan ta'adda

A wani labari na daban, wata mata 'yar asalin Florida mai suna Kris Hedstrom ta maka makwabcinta a kotu tare da bukatar sanin mahaifin akuyoyinta biyar da ta siya a watan Disambar da ta gabata.

Karar da Hedstrom ta cike na bukatar kodai Heather Dayner ya dawo mata da $900 wanda ta biya don siyan wadannin akuyoyin Najeriya a Disamba, ko kuma a yi gwajin kwayar halittar akuyoyin don gano tsatsonsu.

A karar da ta shigar, ta ce tayi tsammanin za ta iya yi wa akuyoyinta rijista ne a kungiyar akuyoyin kasar Amurka.

Hedstorm ta ce: "Dayner, mamallakin gidan gonar Baxter da ke Odessa ya sanar da ni cewa uban akuyoyin yana da rijista a kungiyar amma kuma kungiyar ta ki karbar akuyoyin saboda banbancinsu."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel