SERAP ta ba Buhari wa'adi ya nemo N300m da aka nema aka rasa a asusun gwamnati

SERAP ta ba Buhari wa'adi ya nemo N300m da aka nema aka rasa a asusun gwamnati

Kungiyar SERAP mai fafutikar yaki da yi wa tattalin arziki ta'annati, ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya lalubo wasu makudan kudi da ake zargi sun yi layar zana daga asusun gwamnati.

Kungiyar ta shimfida wa shugaba Buhari wa'adin kwanaki 14 domin ya gaggauta umartar ministan shari'a kuma lauyan koli, Abubakar Malami, gudanar da bincike kan wannan mummunan zargi.

Baya ga ministan shari'a, SERAP ta bukaci shugaban kasar ya umarci duk wasu hukumomi masu ruwa da tsaki kan yaki da yi wa tattalin arziki zagon kasa, da su tsunduma cikin bincike kan naira miliyan 300 da aka nema aka rasa.

SERAP ta bukaci shugaban kasar ya tursasawa ministan shari'a da sauran hukumomi masu yaki da cin hanci su aiwatar da bincike kan annobar rashawa da ta yadu a ma'aikatu, cibiyoyi da hukumomin gwamnati.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari
Hakkin mallakar hoto; Fadar shugaban kasa
Shugaban kasa Muhammadu Buhari Hakkin mallakar hoto; Fadar shugaban kasa
Asali: UGC

A gargadin da kungiyar ta yi, ta ce rahoton bin diddigi da ofishin Odita Janar na kasa ya fitar kan harkokin kudi na shekarar 2017, ya nuna cewa "an barnatar ko an karkatar da akala, ko kuma an sace Naira miliyan 300 daga asusun gwamnati."

A wasikarta mai dauke da kwanan watan ranar 4 ga watan Yuli tare da sa hannun mataimakin shugabanta, Kolawole Oluwadare, ta ce rahoton ya nuna yadda wannan zunzurtun kudade suka sulala ba tare da an yi bayanin yadda aka kashe su ba.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, SERAP ta ce rashin daukar wannan shawarwari da ta bayar zai sabawa dokar yaki da rashawa wadda ke rubuce cikin kundin tsarin mulkin kasa da aka yi wa kwaskwarima a 1999.

KARANTA KUMA: Har yanzu ba a sa ranar bude makarantu ba a Kano - Kwamishinan Ilimi

Kungiyar ta ce bankado duk wasu masu hannu cikin wannan badakala tare da hukunta su, zai taka rawar gani wajen tabbatar da ikirarin da gwamnatin Buhari ta ke yi na yaki da cin hanci da rashawa.

Wasu daga cikin ma'aikatun da ake zargi cikin wannan badakala sun hadar da Ofishin Shugaban Ma'aikatan Gwamnatin Tarayya, Ma'aikatar Harkokin Waje da kuma Ma'aikatar Ruwa.

Sauran sun hadar da; Majalisun Dokoki na Tarayya, Ma'aikatar Shari'a, Hukumar Cibiyar Ilimin Dimokuradiyya da Ayyukan Majalisa, Jami'ar Tarayya ta Albarkatun Man Fetur da sauransu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel