Yadda aka hana ni shiga addu'ar Fida'un marigayi Ajimobi - Mataimakin gwamnan Oyo

Yadda aka hana ni shiga addu'ar Fida'un marigayi Ajimobi - Mataimakin gwamnan Oyo

Mataimakin gwamnan jihar Oyo, Rauf Olaniyan, ya ce iyalan marigayi Gwamna Ajimobi sun san da zuwansa gidansu na Ibadan a ranar Fidaunsa.

An hana Olaniyan shiga rukunin gidajen da ke Oluyole inda zai isa gidan marigayin tsohon gwamnan a ranar Lahadi, The Punch ta ruwaito.

Iyalan marigayin gwamnan ta bakin mai magana da yawunsa, Bolaji Tunji, ya ce iyalan basu san da zuwan mataimakin gwamnan ba.

Amma kuma wata takarda da babban mataimakin na musamman ga mataimakin gwamnan, Omolere Omoetan ya fitar, ya ce iyalan marigayin sun san yana jira a kofar shiga.

"Har a halin yanzu, wasu 'yan gidan da hadimin marigayin suna ci gaba da tsame hannunsu a kan hana mataimakin gwamnan shiga wurin addu'a da aka yi.

"A yau rana ta takwas da rasuwar tsohon gwamnan jihar Oyo, an hana mataimakin gwamna Rauf Olaniyan shiga.

"Mataimakin gwamnan da ya jagoranci sauran wakilan da suka hada da wasu kwamishinoni, an barsu waje suna jira na wurin mintuna 15. Ko bayan da jami'an tsaro suka shiga ciki don sanar da cewa wakilan gwamna suna waje, babu umarnin barinsu shiga da ya biyo baya.

"A wani lokacin, jami'an tsaron sun kara tsanani don har sun nemi rikici da ADC na mataimakin gwamnan. Daga nan ne mataimakin gwamnan ya yanke hukuncin barin wurin.

"Bayan daukar tsawon lokaci don ganin ko za a bar shi shiga amma shiru, ya yanke hukuncin tafiyarsa.

Yadda aka hana ni shiga addu'ar Fida'un marigayi Ajimobi - Mataimakin gwamnan Oyo
Yadda aka hana ni shiga addu'ar Fida'un marigayi Ajimobi - Mataimakin gwamnan Oyo. Hpto daga The Punch
Asali: UGC

KU KARANTA: Maryam Sanda: Yadda wata mata ta yi hayar 'yan bindiga suka kashe mijinta

"Mataimakin gwamnan ya kira Alhaji Kunle Sanni, shugaban kungiyar Musulmi ta jihar Oyo, wanda ke jagorancin addu'ar, amma sai ya ce kanshi a daure yake'. Wannan alama ce da ta nuna cewa an tsara komai," takardar tace.

Kamar yadda ta kara da cewa, "Babu gaskiya da iyalan suka ce basu san da wakilin gwamnatin jihar ba a waje duk da kira da aka dinga yi wa Bolaji Tunji a wurin.

"Hakazalika, wakilan da gwamnan ya tura wurin addu'ar na nuna cewa gwamnan jihar ya dauka marigayin a babban matsayi.

"Mataimakin gwamnan ya kara bayyana cewa, duk da abinda aka yi mishi kuma ya nuna hakurinsa, bai rike kowa da ga cikin iyalan mamacin a zuciya ba. Yana ci gaba da yi wa tsohon gwamnan addu'ar rahama.

"Injiniya Rauf Olaniyan na yin amfani da wannan damar wurin kira ga kwamishinan 'yan sanda jihar a kan rashin kwarewa da rashin da'a da jami'ansa suka nuna."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: