Muna samun nasara a fagen yaki da cutar korona - Ganduje

Muna samun nasara a fagen yaki da cutar korona - Ganduje

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya ce jihar Kano na ci gaba da samun nasarori a fagen yaki da annobar cutar korona a fafutikar da ta ke yi na dakile yaduwarta a fadin jihar.

Babban sakataren yada labarai na fadar gwamnatin Kano, Malam Abba Anwar, shi ne ya bayyana hakan a madadin gwamnan cikin wata sanarwa da ya gabatar a ranar Asabar.

Sanarwar ta bayyana cewa, gwamnan ya yi wannan furuci ne a yayin wani taron manema labarai tare da kwamitin kar ta kwana kan yaki da cutar korona ta gwamnatin jihar ta kafa.

Ganduje ya ce an cimma wannan nasara ne saboda kwazon da yake nunawa da himmar akidarsa ta siyasa wajen jagorantar matakan yaki da cutar COVID-19 a jiharsa.

Ya ce gwamnatin jihar ta mayar da hankali wajen tsananta yi wa mutane gwajin cutar a jihar a cibiyoyin gwaji biyar da gwamnatinsa ta kafa a fadin jihar.

Ya lura cewa, adadin mutanen da ake yi wa gwajin cutar duk rana a fadin jihar, ya zarce adadin da hukumar dakile yaduwar cututtuka a kasa NCDC ta kayyade.

Gwamnan jihar Kano; Abdullahi Umar Ganduje
Hakkin mallakar hoto; Basiru Yusuf Shuwaki @Shuwakiyusuf
Gwamnan jihar Kano; Abdullahi Umar Ganduje Hakkin mallakar hoto; Basiru Yusuf Shuwaki @Shuwakiyusuf
Asali: Twitter

Gwamnan ya ce: "A yayin da Hukumar NCDC ta nemi mu rika yi wa mutum 100 gwajin cutar a duk rana, adadin mutanen da ake yi wa gwaji kullum a jihar a ya zarta hakan."

"Dagewa a kan mayar da hanakali, shi ne ya yi tasiri wajen raguwar adadin mutanen da cutar ta ke harbi a jihar Kano."

Babban jami'i a kwamitin yaki da cutar da gwamnatin jihar Kano ta kafa, Dr. Tijjani Hussaini, ya bayyana cewa, "duk da cibiyoyin gwajin cutar guda biyar da ake da su ajihar Kano, a kan kuma aika da wasu samfurin da aka dauka daga Kano zuwa Abuja domin a yi musu gwajin cutar."

KARANTA KUMA: Sace Yara daga Kano zuwa Kudu: Ganduje ya sake kafa kwamiti na musamman

Ma'aikatar Lafiya ta jihar a ranar Juma'ar da ta gabata ta sanar da cewa, an yi wa mutum 13,727 gwajin cutar tun daga lokacin da ta bulla kawo yanzu.

Haka kuma alkaluman hukumar NCDC sun tabbatar da cewa, mutum 1,264 suka harbu da cutar tun bayan bullarta har kawo yanzu.

Taskar bayanai ta hukumar NCDC a ranar Asabar, 4 ga watan Yuli, ta ce mutum 188 ne kadai suka rage masu da kwayoyin cutar a jihar yayin da tuni an sallami mutum 1,024 daga cibiyoyin killace masu cutar bayan sun samu waraka.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel