Gobara ta ci mutum 16 a Kano

Gobara ta ci mutum 16 a Kano

- A cikin watan Yuni kadai, bala'o'i daban-daban na wutar gobara sun salwantar da rayuka mutum 16 a jihar Kano

- Hukumar kwana-kwana ta sanar da cewa an yi asarar dukiya ta kimanin naira miliyan arba'in cikin wata guda a jihar Kano

Kimanin mutane 16 ne suka rasa rayukansu a sanadiyar musibu na gobara daban-daban da suka auku cikin watan Yuni na shekarar da muke ciki a jihar Kano.

Kakakin hukumar kwana-kwana na jihar, Saidu Muhammed, wanda ya bayyana hakan a karshen makon da ya gabata, ya ce lamarin ya kuma janyo asarar kadarori da darajarsu ta kai naira miliyan 40.6 a cikin wannan lokaci.

Muhammed ya ce, a yayin gudanar da ayyukan agaji da kai dauki da suka rataya a wuyansu, sun samu nasarar ceto rayukan mutane 71 da dukiya wadda ta kai naira miliyan 120 a cikin bala'o'i na gobara 51.

A cewarsa, "Ma'aikatar ta kuma samu kiraye-kiraye na neman kawo dauki har sau hamsin, yayin da kuma aka yi musu kira na karya guda 9 daga mazauna gari."

Masu aikin kashe gobara
Hoto daga; Jaridar Tribune
Masu aikin kashe gobara Hoto daga; Jaridar Tribune
Asali: UGC

"Ya alakanta aukuwar wannan bala'o'i na gobara da hatsarin mota, amfani da kayayyakin lantarki da makamashin gas ko fetur."

"Ya kuma shawarci mazauna jihar da su yi taka tsantsan yayin amfani da kayayyakin lantarki don kauce wa aukuwar gobara," inji Muhammed.

Legit.ng ta ruwaito cewa, watanni biyu da suka gabata, 'yan gudun hijira 14 ne suka rasa rayukansu yayin da 15 daga ciki suka samu raunika daban-daban.

KARANTA KUMA: Coronavirus: Jihohi 20 da suka zaftare naira tiriliyan 1.4 daga kasafin kudin bana

Hakan ya faru ne sakamakon barkewar gobara a sansanin 'yan gudun hijarar da ke karamar hukumar Ngala ta jihar Borno a Arewa maso Gabashin Najeriya.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta bayyana, gobarar ta fara ne da karfe 2:15 na Yammacin ranar Alhamis, 16 ga watan Afirilun 2020.

Kamar yadda wata majiya ta tabbatar, jami'an hukumar kwana-kwana sun yi iyaka bakin kokari wajen kashe wutar da gaggawa.

Majiyar ta shaidawa manema labarai cewa, gobarar ta lamushe akalla gidaje 1250 a sansanin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel