Kano: Hukuma ta fara takawa ma su wakokin begen Annabi birki

Kano: Hukuma ta fara takawa ma su wakokin begen Annabi birki

Hukumar da ke da alhakin tace fina - finai da wakoki a jihar Kano ta ce ba za a kara sakin wata wakar begen Annabi ba sai da izininta, a saboda haka za a bawa sha'irai lasisi.

Muhammad Na'abba, shugaban hukumar, ne ya sanar da hakan ranar Talata yayin wata tattaunawarsa da sashen Hausa na BBC.

Na'abba, wanda aka fi sani da 'Afakallah', ya ce hukumarsa ta dauki wannan mataki ne saboda sakin layin da wasu sha'irai ke yi da sunan wakokin begen Annabi.

A cewar Afakallah, za su tantance sha'irai tare da basu lasisi, kuma koda an bawa sha'iri lasisi sai an tace wakarsa domin tabbatar da babu batanci a cikinta kafin ta shiga gari.

Afakallah ya bayyana cewa aikin hukumarsa bai tsaya ga iya fina - finai da wakokin nanaye ba.

Ya bayyana cewa an kafa hukumar ne domin ta gudanar da aiyuka guda uku da suka hada da; kyautata zamantakewa, tabbatar da girmama addini da kuma al'ada.

Kano: Hukuma ta fara takawa ma su wakokin begen Annabi birki
Gwamnan Kano; Dakta Abdullahi Umar Ganduje
Asali: Twitter

Shugaban ya bayyana cewa ko kadan basa jin dadin yadda wasu sha'irai ke cin zarafin Allah da manzonsa da sauran wasu manya ma su daraja duk da sunan yabo ko bege.

"Mun bawa wasu jagororin sha'irai damar tace wakokin bege kafin a sakesu, amma sai lamarin ya zama rigima, a saboda haka sai mu ka dawo da aikin wurinmu, tunda dama can aikinmu ne.

"Ana shiga hurumin Allah da manzonsa tare da zagin wasu manyan mutane ma su daraja kuma 'wai' duk da sunan yabo," a cewar Afakalla.

DUBA WANNAN: Kamar a fim: Yadda jiragen yakin sojoji suka dinga ruwan wuta a wasu maboyar Boko Haram

Da ya ke magana a kan irin wasu wakokin bege da ba su dace ba, Afakallah ya bayyana cewa a baya an yi wasu wakokin yabo da suka haifar da barkewar tarzoma a birnin Kano.

Ya kara da cewa gwamnati ta farga kuma za ta yi wa tufkar hanci saboda mutanen Kano sun kasance ma su riko da addini, kuma za su iya daukan doka a hannunsu matukar gwamnati ba ta dauki matakin da ya dace ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel