Jerin gwamnoni 7 da suka kamu da cutar Coronavirus, 4 sun warke (Hotuna)
Bayan watanni hudu da bullar cutar Coronavirus a Najeriya, Akalla gwamnoni 7 sun kamu da cutar.
Adadin wadanda suka kamu da cutar kawo yammacin Juma'a sun kai 27,564 bisa alkaluman hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya wato NCDC.
Cutar ta yadu cikin mutane daban-daban wanda ya hada da yan siyasa, malaman addini, manyan yan kasuwa, Likitoci, Malaman jinya, da sauran su.
Ga jerin gwamnonin bakwai da Korona ta harba.
1. BALA MOHAMMED: Ya kwashe kwanaki 15 a killace
Gwamnan jihar Bauchi, Bala AbdulKadir Mohammed, ne gwamnan farko da ya kamu da cutar COVID-19.
A ranar 24 ga Maris, hadiminsa, Mukhtar Gidado, ya saki jawabin cewa gwamnan ya killace kansa. Amma ranar 9 ga Afrilu gwamna ya warke.

Asali: Twitter
2. NASIR EL-RUFAI: Ya kwashe makonni 3 a killace
Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i ne gwamna na biyu da cutar a Najeriya. Hakazalika shine mutumin farko da ya kamu da cutar a jiharsa.
A faifan bidiyon da ya saki ranar 28 ga Maris, gwamnan ya sanar hakan.

Asali: Facebook
3. SEYI MAKINDE: Ya warke cikin kasa da mako daya
A ranar 30 ga Maris, gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya sanar da cewa ya killace kansa bayan kamuwa da cutar Coronavirus.

Asali: Facebook
4. IKEAZU IKPEAZU: Ya warke bayan kimanin wata daya
Gwamnan jihar Abia, Ikpeazu ya sanar da cewa ya kamu da cutar ranar 8 ga Yuni, 2020.
Bayan kimanin wata daya, gwamnan ya warke ranar Asabar, 4 ga watan Yuli.

Asali: UGC
5. IFEANYI OKOWA
Gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa ya kamu da cutar Corona tare da matarsa, Edith, da daya cikin 'yayansa mata.
Har yanzu suna jinya

Asali: Twitter
6. ROTIMI AKEREDOLU
A ranar Talata, gwamnan jihar Ondo, ya sanar da cewa ya kamu da cutar COVID-19. Amma Akeredolu ya bayyana cewa duk da cewa yana killace, ba zai mika ragamar mulki hannun mataimakinsa ba.
Har yanzu yana jinya

Asali: Twitter
7. David Umahi
Gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi, ne gwamnan karshe da ya kamu yanzu. Ya sanar da kamuwarsa da cutar ne a yau Asabar.
Hakazalika ya sanar da cewa ya wasu daga cikin hadimansa sun kamu da cutar.

Asali: Twitter
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng