Albashina a baya ya fi wanda na ake bani a matsayin minista – Pantami

Albashina a baya ya fi wanda na ake bani a matsayin minista – Pantami

Ministan Sadarwa, Isa Pantami ya ce albashinsa da allawus a matsayin minista bai kai abinda ya ke samu ba a lokacin da ya ke aiki a matsayin malami a Jami'ar Kasa da Kasa ta Madina a kasar Saudiyya.

Pantami ya furta wannan ne yayin da ya ke martani a kan rahotonin da wasu jaridun intanet suka wallafa na cewa ya siya manyan gidaje uku a cikin shekara guda tun bayan zamansa minista.

A cewar sanarwar da mai magana da yawunsa, Uwa Suleiman ya fitar a rana Juma'a, ministan ya ce ya dawo Najeriya ne don "amsa kirar da aka masa ne neman ya zo ya yi wa kasarsa hidima."

Albashina a baya ya fi wanda na ake bani a matsayin minista – Pantami
Albashina a baya ya fi wanda na ake bani a matsayin minista – Pantami
Asali: UGC

DUBA WANNAN: An yi wa wani jirgin UN ruwan harsashi a Borno

Wani sashi daga cikin sanarwar ta ce, "Domin kawar da shakku daga zukutan mutane, Hon Minista bai taba siyan ko da gida daya ba a ko ina a duniya tun lokacin da ya kama aiki a matsayin minista.

"Daga daga cikin gidajen da aka wallafa, gidansa ne da ya ke ciki tun Janairun 2017, fiye da shekara biyu kafin ya zama minista yayin da daya kuma gidan haya ne da ya karba ranar 17 Disamban 2019. Sauran hotunan gidajen biyu kuma bai san inda aka samo su ba.

"Yana da kyau a sani cewa albashi da allawus dinsa a matsayin minista ba su kai abinda ya ke samu ba a lokacin da ya ke aiki a matsayin Farfesa a Jamiar Kasa da Kasa ta Madina a Saudiyya, inda shine dan Najeriya na farko da ya fara koyarwa a wannan matsayin.

"Ya dawo gida Najeriya ne kawai saboda kishin kasa da shaawar ganin ya bayar da gudunmuwarsa wurin cigaban kasa.

"Dr Pantami yana daga cikin tsirarun yan Najeriya da abin duniya ba ya tsole musu ido sai dai kishin kasa da son yi wa alumma hidima kamar yadda za a iya gani a lokacin da ya amsa kirar da aka yi masa na zuwa ya yi wa kasarsa aiki."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel