Cikin mako daya, fiye da mutane milyan uku daya sun yi rijistan neman aikin N-Power

Cikin mako daya, fiye da mutane milyan uku daya sun yi rijistan neman aikin N-Power

Akalla matasa milyan uku sukayi rijistan neman aiki a shirin N-Power na gwamnatin tarayya cikin mako daya kacal, lissafi daga shafin rijistan ya nuna.

The Nation ta ce hakan na kunshe cikin jawabin da mataimakiyar diraktan ma'aikatar kan yada labarai, Rhoda Iliya, ta saki ranar Juma'a a Abuja.

Ma'aikatar walwala, tallafi da jin dadin al'umma ta kaddamar da shirin daukan sabbin matasa karo na uku a shirin N-Power ranar 26 ga watan Yuni, 2020.

Mako daya bayan bude shafin rijistan, ma'aikatar ta ce sama da mutane milyan uku sukayi rijista.

Gwamnati ta ce mutane 400,000 za'a dauka a wannan sabon daukan.

Hakan ya na nufin a kusan mutane 10,080 su ke rububin wannan aiki a cikin kowane minti guda, hakan ya na nufin a kowace sa’a, matasa 604,800 su ke cike sunayensu a shafin neman aikin.

Cikin mako daya, fiye da mutane uku daya sun yi rijistan neman aikin N-Power
Cikin mako daya, fiye da mutane uku daya sun yi rijistan neman aikin N-Power
Asali: UGC

KU KARANTA: Yadda jami'an NCDC sukayi rikici da wani mai Korona da akayi kokarin kaiwa cibiyar killacewa (Bidiyo)

Za ku tuna cewa a ranar Lahadi, 28 ga watan Yuni, gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana mutane fiye da miliyan guda sun yi rijista cikin kwanaki biyun farko.

Hakan na zuwa ne bayan rade-radin cewa an yi wa shafin aikin kutse.

Makonni biyu da suka gabata mun kawo muku rahoton cewa Ministar walwala da jin dadin al'umma, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta bayyana cewa za'a sallami matasan N-Power da aka dauka a shekarar 2016 wannan watan na Yuni, 2020.

Hakazalika za'a sallami wadanda aka dauka a 2018 a watan Yuli, 2020.

Shirin N-Power ya dauki matasa 500,000; karon farko an debi mutane 200,000 a Satumba 2016, sannan 300,000 a watan Agustan, 2018.

A lokacin da aka daukesu aiki, an bayyana musu cewa watanni 24 za suyi amma matasa 200,000 farko da aka dauka sun kwashe sama da watanni 40.

Matasan sun ce basu ki a sallamesu ba, amma a biyasu kudin albashin watanni biyu da ba'a biyasu ba har yanzu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng