Gwamna Ikpeazu ya warke daga cutar korona

Gwamna Ikpeazu ya warke daga cutar korona

Gwamnan jihar Abia, Okezie Ikpeazu ya warke daga COVID-19 wato cutar korona.

Sakamakon gwajin da aka yi masa ranar Juma'a 3 ga watan Yuli ya nuna baya dauke da kwayar cutar.

Gwamnan ya killace kansa ne tun ranar 8 ga watan Yunin 2020 a lokacin da aka gano ya kamu da cutar.

Sanarwar warkewar gwamnan ta fito ne daga bakin Kwamishinan watsa labarai na jihar, Okiyi Kalu kamar yadda LIB ta ruwaito.

Gwamna Ikpeazu ya warke daga cutar korona
Gwamna Ikpeazu ya warke daga cutar korona
Asali: Original

DUBA WANNAN: An yi wa wani jirgin UN ruwan harsashi a Borno

Sanarwar ta ce, "Dukkan godiya ta tabbata ga Allah, gwajin da Hukumar Kiyaye Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Ƙasa, NCDC ta yi a kan samfurin Gwamna Okezie Ikpeazu a ranar Alhamis 2 ga watan Yulin 2020 ya fito a ranar Juma'a 3 ga watan Yulin 2020 kuma baya ɗauke da ƙwayar cutar.

Hakan na nufin Gwamna Ikpeazu ya warke daga cutar kamar yadda dokokin NCDC da Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, suka tanadar.

Mun gode."

A wani labarin daban, kun ji cewa Eunice Ortom, matar gwamnan jihar Benue, ta kamu da kwayar cutar COVID-19 da aka fi sani da coronavirus kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Matar gwamnan da fitar da sanarwar hakan a daren ranar Juma'a inda ta ce dan ta da wasu maaikatanta suma sun kamu da cutar.

Ta shawarci dukkan wadanda suka gana da ita a baya bayan nan su killace kansu kuma su tafi ayi musu gwajin na COVID-19.

Eunice ta ce kamuwa da cutar baya nufin mutum zai mutu tare da cewa tana fitar dan ta da ita za su warke.

"A daren yau, na samu sakamakon gwajin da hukumar NCDC ta yi min a kamar yadda aka saba yi a gidan gwamnati a Makurdi kuma sakamakon ya nuna ni da da na da wasu maaikata na mun kamu," a cewar sanarwar.

"A halin yanzu mun killace kan mu kamar yadda kaidar cutar ta ke kuma za mu fara shan magunguna a karkashin kulawar likitoci.

"Duk da cewa na kira dukkan wadanda na san na yi cudanya da su na fada musu su tafi gwaji, ina shawartar duk wanda ya yi cudanya da ni cikin makonni biyu da suka gabata ya tafi a gwada shi.

"Ina son tunatar da mutane cewa COVID-19 ba ya nufin mutuwa duba da adadin mutanen da ke warkewa kawo yanzu saboda haka kowa ya kwantar da hankalinsa amma akwai bukatar mu cigaba da kulawa.

"Ina shawartar mutane su cigaba da kiyaye kansu da bin dokokin hukumomin lafiya. Ku kasance lafiya! COVID-19 gaskiya ne!."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel