An kashe mana mutane 99 a kudancin Kaduna - Fulani Makiyaya

An kashe mana mutane 99 a kudancin Kaduna - Fulani Makiyaya

- Rikici tsakanin Fulani Makiyaya da kabilun kudancin Kaduna ya ki ci, ya ki cinyewa

- An yi asarar daruruwan rayuka da dukiyoyi sakamakon wannan rikici

- Gwamnan jihar Kaduna ya bada umurnin binciken abinda ya sabbaba rikicin Zangon Kataf na shekarar 1992.

Shugabannin al'ummar Fulani mazauna kudancin Kaduna, karkashin jagorancin gamayyar kungiyoyin Fulani Makiyaya, sun bayyana cewa an hallaka musu akalla rayuka 99.

Sun bayyana cewa an kashe musu wannan adadin mutanen ne a watan Yuni a karamar hukumar Zangon Kataf da Kaura.

Sun kara da cewa wasu matasan kabilar Atyap da Tsam dake Zangon Kataf da Kaura ne suka aikata wadannan aika-aikan na kashesu, sace musu dukiya, da lalata musu muhalli.

Wakilin gamayyar Fulanin wanda yayi hira da manema labarai a Kaduna ranar Juma'a ya zargi kungiyar al'ummar mutan kudancin Kaduna SOKAPU da hannu cikin kisan jama'ar Fulani.

Sakataren kungiyar Mobgal Fulbe, Nuhu Ibrahim, ya ce bayan Fulani 139 da aka nema aka rasa, an gona musu gidaje.

Amma kungiyar SOKAPU ta ce ba tada masaniya game da kisan Fulani makiyaya 99 a kudancin Kaduna.

Kakakin kungiyar SOKAPU, Luka Binniyat, ya bayyanawa jaridar Punch cewa, "A saninmu babu abinda ya faru a Zangon-Kataf. Bamu da masaniya game da wani harin da aka kaiwa Fulani a kauyukan Atyap."

Duk yunkurin da aka yi na ji daga bakin kakakin hukumar yan sandan jihar, Mohammed Jalinge, ya ci tura.

An kashe mana mutane 99 a kudancin Kaduna - Fulani Makiyaya
An kashe mana mutane 99 a kudancin Kaduna - Fulani Makiyaya
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Gwamnan jihar Ebonyi ya kamu da cutar Coronavirus

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel