Rigima a kan mahaifin akuyoyi: Mai akuya ta maka makwabcinta a kotu

Rigima a kan mahaifin akuyoyi: Mai akuya ta maka makwabcinta a kotu

Wata mata 'yar asalin Florida mai suna Kris Hedstrom ta maka makwabcinta a kotu tare da bukatar sanin mahaifin akuyoyinta biyar da ta siya a watan Disambar da ta gabata.

Karar da Hedstrom ta cike na bukatar kodai Heather Dayner ya dawo mata da $900 wanda ta biya don siyan wadannin akuyoyin Najeriya a Disamba, ko kuma a yi gwajin kwayar halittar akuyoyin don gano tsatsonsu.

A karar da ta shigar, ta ce tayi tsammanin za ta iya yi wa akuyoyinta rijista ne a kungiyar akuyoyin kasar Amurka.

Hedstorm ta ce: "Dayner, mamallakin gidan gonar Baxter da ke Odessa ya sanar da ni cewa uban akuyoyin yana da rijista a kungiyar amma kuma kungiyar ta ki karbar akuyoyin saboda banbancinsu."

Ta ce kungiyar ta bukaci ta kawo gashi 40 na mahaifin akuyoyin don tabbatar da tsatsonsu, hakan yasa ta tura bukatar neman sakamakon gwajin DNA na akuyoyin.

Dayner ya yi martani inda yace zai karba akuyoyin tare da mayar wa Hedstorm kudinta.

Dayner ya ce Hedstrom ta tsallake komai inda ta kira mishi 'yan sanda, jaridar The Nation ta ruwaito.

Rigima a kan mahaifin akuyoyi: Mai akuya ta maka makwabcinta a kotu
Rigima a kan mahaifin akuyoyi: Mai akuya ta maka makwabcinta a kotu. Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Rayuwata ta sauya tunda matata ta fara hana ni hakkina - Magidanci

A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan jihar Sokoto ta kama wani mutum mai suba Shuaibu Aliyu sakamakon zarginsa da ake da dirkawa yarinya mai shekaru 14 ciki tare da yadda jaririyar da ta haifa a daji.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, CP Sani Kaoje ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai bayan kama masu laifi.

Ya ce an damke wanda ake zargin da laifin fyade da kuma yunkurin kisan kai. Kaoje ya bayyana cewa, "wani Alhaji Hamisu Abubakar da ke yankin Kalambaina a karamar hukumar Wamakko ta jihar Sokoto ya kai korafi ofishin 'yan sanda.

"Ya ce wani mutum mai suna Shuaibu Aliyu ya ja yarinya mai shekaru 14 cikin dakinsa inda yayi mata fyade."

Ya kara da cewa, "Sakamakon hakan, ta samu ciki har ta haihu. Ta kai wa wanda ake zargin jinjirin tare da wani abokinsa Nasiru Attahiru wanda yanzu ake name.

"Sun karba tare da jefar da jinjirin a wani daji da ke kauyen Gidan Boka a karamar hukumar Wamakko ta jihar Sokoto."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel