Sabbin mutum 454 sun kamu da cutar korona a Najeriya

Sabbin mutum 454 sun kamu da cutar korona a Najeriya

Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa a Kasa (NCDC) ta ce annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 454 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NCDC ta fitar da misalin karfe 11.52 na daren ranar Juma'a 3 ga Yulin shekarar 2020.

A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa karin sabbin mutum 454 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka;

Sabbin mutum 454 sun kamu da cutar korona a Najeriya
Sabbin mutum 454 sun kamu da cutar korona a Najeriya
Asali: Twitter

Lagos-87

Edo-63

FCT-60

Ondo-41

Benue-32

Abia-31

Ogun-29

Oyo-19

Kaduna-17

KU KARANTA: Zaben Edo: APC ta tura Ganduje, PDP ta tura Wike

Delta-16

Enugu-15

Borno-14

Plateau-9

Nasarawa-8

Kano-5

Bauchi-4

Gombe-2

Katsina-1

Kogi-1

Alkalluman da hukumar ta dakile cututtukan ta fitar a ranar Juma'a 3 ga Yulin shekarar 2020 ya nuna cewa jimillar wadanda suka kamu da cutar ta korona a kasar 27,564.

An sallami mutum 11,069 bayan an tabbatar da sun warke sarai, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 628.

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, Darekta janar na hukumar NCDC na kasa, Dr. Chikwe Ihekweazu, ya ce matasa masu shekaru 20 zuwa 40 ne su ke taimakawa wajen yada kwayar cutar COVID-19 a Najeriya.

Da ya ke magana da ‘yan jarida domin bayyana inda kwamitin yaki da COVID-19 a Najeriya watau PTF ta kwana, Dr. Chikwe Ihekweazu, ya ce masu matsakaitan shekaru ne su ke yawo da cutar.

Chikwe Ihekweazu ya kuma bayyana cewa manyan mutane da su ka haura shekaru 50 ne su ka fi mutuwa daga cutar Coronavirus mai kawo sarkafewar numfashi.

Zuwa yau Juma’a da mu ke hada wannan rahoto, akwai mutane fiye da 27, 000 da su ka kamu da cutar a Najeriya.

Bayan haka akalla mutane 603 ne su ka mutu a sanadiyyar COVID-19. “Yayin da mutane su ke cigaba da kamuwa da cutar a fadin Duniya kamar yadda babu mamaki ku ke gani.

Ya na kara fitowa karara cewa cutar ta fi yawo a cikin yara; matasa masu shekara 20 zuwa 40, ba kananan yara ba.”

Dr. Ihekweazu ya cigaba: “Kuma su na zagayawa da wannan kwayar cuta. Amma a karshe wadanda su ke mutuwa a sanadiyyar cutar, manyan mutane ne wadanda su ka zarce shekara 50.”

“Saboda haka, dole mu kara kokari gaba dayanmu wajen kare lafiyar dattawanmu.” Inji Ihekweazu.

Ihekweazu ya ja-kunnen ‘yan Najeriya da su guji tafiyar da ba ta zama dole ba zuwa cikin wasu jihohin. Hakan zai taimaka wajen rage yaduwar wannan cuta a Najeriya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel