Ban mallaki gida ko daya a duniya ba tun da na hau Minista - Dr Isa Pantami ya yi martani

Ban mallaki gida ko daya a duniya ba tun da na hau Minista - Dr Isa Pantami ya yi martani

Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Sheikh Dakta Isa Obrahim Ali Pantami, ya yi watsi da rahotannin wata kafar yada labarai a yanar gizo da ta yi ikirarin cewa ya sayi sabbin gidaje da ajiye iyalinsa.

Ministan ya yi hakan ta bakin mai magana da yawunsa, Uwa Suleiman, da yammacin Juma'a, 3 ga watan Yuli, 2020.

Ta ce ya kamata a sani cewa kudin albashin da Malam Pantami ke samu a yanzu matsayin minista bai kai kudin da yake samu lokacin da yake karantarwa a jami'ar Madina ba.

Hakazalika ba duniya ke gabbansa ba kawai ya dawo Najeriya ne domin taimakawa cigaban kasa.

Jawabin yace: "Dr Isa Pantami na daya daga cikin yan tsiraru a Najeriya da duniya bata damesu ba, kawai kishin kasa da sadukar da kai ya sanya ya amsa kira dawowa gida.

Kawai dan fayyace gaskiya, Ministan bai sayi gida ko daya ba a duniya tun lokacin da ya hau Minista."

"Daya daga cikin gidajen da aka wallafa wanda ministan ya ke zama ne tun Junairun 2017, sama da shekaru biyu kafin zama minista.

Dayan gidan kuma haya ya karba tun daga ranar 17 ga Disamban 2019."

Jaridar Sahara Reporters ce ta wallafa hotunan wasu manya gidaje da ta ikirarin cewa Ministan Sadarwa, Dakta Isa Pantami, ya ajiye matansa uku a Abuja.

Jaridar ta ce Ministan na shagalinsa a Abuja.

Kalli hotunan gidajen:

Ban mallaki gida ko daya a duniya ba tun da na hau Minista - Dr Isa Pantami ya yi martani
Credit: Sahara Reporters
Asali: Facebook

KU KARANTA: Hukumar Sojin sama ta samu sabon jirgin yaki ATR-42 na leken asiri

Ban mallaki gida ko daya a duniya ba tun da na hau Minista - Dr Isa Pantami ya yi martani
Credit: Sahara Reporters
Asali: Facebook

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel