Zaben Edo: APC ta tura Ganduje, PDP ta tura Wike

Zaben Edo: APC ta tura Ganduje, PDP ta tura Wike

Kwamitin gudanarwa na kasa, NWC, na jamiyyar Peoples Democratic Party, PDP, ta nada Gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Wike a matsayin shugaban kwamitin yakin cin zaben gwamnan jihar Edo.

Jamiyyar ta kuma nada gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri a matsayin mataimakin rundunar cin zaben gwamnan.

Sakataren jamiyyar na kasa, Kola Ologbondiyan ne ya bayar da wannan sanarwar a ranar Jumaa a sahihin shafin Twitter na jamiyyar.

“NWC na @OfficialPDPNig ta nada @GovWike a matsayin shuganan rundunar cin zaben gwamnan jihar Edo. Mataimakinsa kuma shine Rt. Hon. Ahmadu Fintiri," kamar yadda ya wallafa a Twitter.

Zaben Edo: APC ta tura Ganduje, PDP ta tura Wike
Zaben Edo: APC ta tura Ganduje, PDP ta tura Wike. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: UGC

KU KARANTA: An kama wani mutum da ya yi wa 'yarsa ciki a Adamawa

Dan takarar jamiyyar, Gwamna Godwin Obaseki zai fafata da Osagie Ize Iyamo na All Progressives Congress da wasu yan takarar na wasu jamiyyu da za su fafata a zaben na ranar 19 ga watan Satumban a jihar.

Ologbondiyan ya ce, "Duba da cewa mutane jihar Edo suna tare da PDP da Obaseki, ba za su amince wani ya zo ya nemi sauya wa mutanen abinda suke so ba."

A wani labarin daban, Jami'yyar PDP ta yi watsi da karin kudin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi daga N123 zuwa N143.80 duk lita.

A cikin sanarwar da sakataren jamiyyar na kasa, Kola Ologbondiyan ya fitar a ranar Laraba ya bayyana karin kudin man a matsayin, "hukunta yan Najeriya ne duba da matsin tattalin arzikin da ake fama da shi a kasar."

"Jami'yyar ta ce babu dalilin yin karin kudin duba da cewa farashin danyen mai ya fadi a kasuwan duniya wadda hakan ya nuna rashin gaskiyar jamiyyar ta APC," in ji Ologbondiyan.

Ya kara da cewa, "Karin kudin man fetur da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta bayar da umurnin yi a lokacin da yan Najeriya ke fama da rashin kudi saboda annobar korona ya nuna rashin tausayawa halin da yan kasar ke ciki."

Jami'yyar ta yi ikirarin cewa matakan da gwamnatin APC ta dauka ya nuna dama ba ta damu da talakawa ba sai dai kara dilmiya su cikin bakar wahala da talauci.

Ta kuma zargi gwamnati mai ci yanzu da bannatar da kudade wurin gudanar da ayyukan gwamnati a kan wasu tsiraru a maimakon yi wa 'yan Najeriya hidima.

A cewar jami'yyar ta PDP, gwamnati mai ci yanzu ta mayar da Najeriya babban birnin talauci na duniya kuma ta kara tabarbara lamarin ta hanyar yin karin kudin man fetur a maimakon nemo hanyoyin magance matsalar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164