Shugaban ma'aikatan gwamna Lalong ya kamu da cutar Coronavirus

Shugaban ma'aikatan gwamna Lalong ya kamu da cutar Coronavirus

Noel Donjur, Shugaban ma'aikatan gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong, ya kamu da cutar Coronavirus, rahoton Daily Trust ya bayyana.

Hakan ya biyo bayan gwajin da aka yiwa mambobin majalisar zartaswar jihar ne a ranar 1 ga Yuli, 2020 bisa umurnin da gwamna Simon Lalong ya bada.

A jawabin da kwamishanan labaran jihar, Dan Manjang, ya saki, ya ce sakamakon gwajin ya nuna cewa dukkan sauran mambobin majalisar basu kamu da cutar ba illa shugaban ma'aikatan fadar.

Ya ce jami'an kiwon lafiya sun fara kula da shi a daya daga cikin cibiyoyin killace masu cutar a Jos, yayinda aka fara gudanar da gwaji kan iyalansa.

Hakazalika sauran hadiman gwamnan, sakatarorin din-din-din, shugabannin ma'aikatu, manyan jami'an gwamnatin jihar sun yi gwaji kuma suna sauraron sakamakonsu.

Shugaban ma'aikatan gwamna Lalong ya kamu da cutar Coronavirus
Shugaban ma'aikatan gwamna Lalong ya kamu da cutar Coronavirus
Asali: UGC

KU KARANTA: Duk wanda yayi atishawa cikin jirginmu kawai zamu daukeshi mai Korona - Aero

A ranar Laraba, Legit ta kawo muku rahoton cewa Gwamnan jihar Plateau, Simon Bako Lalong, da wasu mambobin majalisar zartarwas sa sun shiga killace kansu bayan kwamishanan masana'antu da kasuwanci, Abe Aku, ya kamu da cutar Coronavirus.

Kwamishanan labaran jihar, Dan Manjang, ya bayyana hakan ne a takardar da ya saki ranar Laraba.

A cewarsa, Lalong ya umurci dukkan kwamishanoninsa su garzaya a yi musu gwajin cutar ta COVID-19.

Watanni shida da bullar cutar Korona a duniya, sama da mutane miliyan goma sun kamu da cutar kuma akalla 500,000 sun rasa rayukansa, lissafin jami'ar Johns Hopkins ya nuna.

Shugaban kungiyar kiwon lafiyan duniya WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce har yanzu duniya bata ga komai game da cutar ba tukun saboda mutane da yawa zasu sake kamuwa muddin gwamnatoci basu dau matakin kwarai ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel