Yanzu-yanzu: Gwamnan Bauchi ya dakatar da Sarkin Misau

Yanzu-yanzu: Gwamnan Bauchi ya dakatar da Sarkin Misau

Gwamman jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya sanar da dakatar da Sarkin Misau, Alhaji Ahmed Suleiman sakamakon rikicin da ya afku a gundumar Hardawa a karamar hukumar Misau da ya yi sanadin mutuwar mutum 9.

Wasu mutane da dama sun jikatta sakamakon rikicin kamar yadda The unch ta ruwaito.

Bayan sarkin, an kuma dakatar da Hakimin Chiromah da Dagajin Kauyen Zadawa ko wakilinsa.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewa an kashe mutum tara yayin da wasu da dama suka jikkata a ranar Litinin bayan rikicin da ya barke tsakanin makiyaya da Fulani manoma a kauyen Zadawa da ke karamar hukumar Misau na jihar Bauchi.

Yanzu-yanzu: Gwamnan Bauchi ya dakatar da Sarkin Misau
Yanzu-yanzu: Gwamnan Bauchi ya dakatar da Sarkin Misau. Hoto daga The Punch
Asali: UGC

KU KARANTA: Yadda 'yan Boko Haram ke samun makamai – Majiya daga Rundunar Soji

Wasu mutane da dama sun tsira da raunika daban daban.

Gwamnan a ranar Talata, ya dakatar da Shugaban karamar hukuma na riko na karamar hukumar Misau, Yaro Gwaram.

Bayan shugaban karamar hukumar, an kuma dakatar da mataimakinsa, Baidu Kafin Misau da Sakatarensa, Usman Abdu.

Rikicin ya samo asali ne saboda fada da ake yi a kan mallakar wani fili inda makiyaya suke kuma sun dade suna kiwo a wurin duk da cewa filin na gwamnati ne.

Karamar hukuma ta mayar da filin gona amma hakan bai yi wa makiyayan dadi ba.

Ku saurari karin bayani ...

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel