Bashin da ake bin Najeriya ya haura N28.63 Trillion - Ofishin kula da basussukan Najeriya

Bashin da ake bin Najeriya ya haura N28.63 Trillion - Ofishin kula da basussukan Najeriya

Jimillan bashin kudin da ake bin Najeriya ya haura Naira Tiriliyan 28,63 (N28.63tn), ofishin kula da basussukan Najeriya DMO ta alanta ranar Alhamis.

A rahoton basussukan kasar da aka saki a daren alhamis, ofishin DMO ta yi bayanin cewa jimillar bashin da ake bin Najeriya ya tashi daga N27.4tn a Disamban 20019 zuwa N28.63tn a Maris 2020.

Hakan ya nuna cewa cikin watanni uku , bashin da Najeriya ta ci ya karu da N1.23tn.

Yayinda N9.99tn daga ciki bashin da aka karbo daga kasashen waje ne, N18.64tn aka karba daga hannun bankunan cikin gida.

Bashin da ake bin Najeriya ya haura N28.63 Trillion - Ofishin kula da basussukan Najeriya
Lissafin bashin Najeriya na bara (2019)
Asali: UGC

KU KARANTA: Duk wanda yayi atishawa cikin jirginmu kawai zamu daukeshi mai Korona - Aero

Rahoton da ofishin DMO ya kara nuna cewa Najeriya ta kashe N609.13 billion wajen biyan wani sashen basussukan tsakanin watan Junairu zuwa Maris, 2020.

Lissafin wata-wata ya nuna cewa an biya N251.35 billion a Junairu, N158.12 billion a Febrairu, kuma N199.658 billion a watan Maris.

A cikin wadannan watanni uku, kudin shigan da gwamnatin tarayya ta samu shine N950.56 billion amma ciki an yi amfani N943.12 billion wajen biyan bashi.

Za ku tuna cewa kungiyar kudin lamunin duniya IMF ta ce Najeriya za tayi amfani da dukkan kudaden shigan da zata samu a shekarar 2020 wajen biyan kudin ruwan bashi.

Duk da haka, Ministocin Kudi, Zainab Ahmed; Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola; Karamin Ministan Sufuri, Gbemisola Saraki da Direktan Ofishin Bashi (DMO), Patience Oniha sun bayyana dalilan da yasa gwamnatin Najeriya ke karbar bashi.

Sun bayyana cewa ya zama dole gwamnati ta cigaba da karbo bashi domin gudanar da ayyukan da al'umma ke bukata tare da cewa ya zama dole a cigaba da karbar bashin.

Sun bayyana hakan ne yayin da suka gana da kwamitin majalisar dokoki na tarayya kan bashi da tallafi domin kare bukatar karbo bashi na $22.718 biliyan da Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatarwa Majalisar Dattawa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel