Yanzu-yanzu: Gobara ta tashi a ofishin CBN dake jihar Gombe
Goabara ta tashi a babbar bankin Najeriya dake jihar Gombe ranar Juma'a, 3 ga watan Yuli, 2020.
Sahara Reporters ta sami rahoto daga majiya cewa gobarar ta fara ci ne misalin karfe 10 na safe.
Wannan ya shiga jerin gobara da aka samu a ma'aikatun gwamnati a fadin tarayya cikin yan watannin nan.

Asali: Original
A baya Legit.ng Hausa ta kawo muku jerin ofishoshin gwamnati biyar da suka zalzala cikin wata daya.
1. Ofishin akawunta janar (Gidan baitul mali)
A ranar 8 ga Afrilu, 2020, Ginin da aka fi sani da 'Gidan baitul mali' wato Treasury House' na kusa da hedkwatar hukumar yan sandan Abuja, a unguwar Garki ya yi gobara.
2. Hedkwatar hukumar CAC
A ranar 15 ga Afrilu, Gobara ta tashi a hedikwatar hukumar yi wa kasuwanci rijista ta kasa (CAC) da ke unguwar Maitama a birnin tarayya, Abuja.
Gobarar ta babbake hawa na karshe a ginin ofishin hukumar CAC mai bene hawa bakwai, tare da lalata muhimman kayayyaki.
3. Hedkwatar INEC dake Abuja
A ranar 17 ga watan Afrilu, Hedkwatar hukumar gudanar da zabe ta kasa watau INEC dake birnin tarayya Abuja ya ci da wuta.
4. Ofishin babban bankin Najeriya CBN
A ranar 21 ga Afrilu, an samu gobara a ofishin babban bankin Najeriya CBN, reshen Jos, jihar Plateau. Bankin ta tabbatar da hakan a shafinta na Tuwita inda ta bayyana cewa tuni an kashe wutar.
5. Hedkwatar NIPOST
A ranar 20 ga watan Mayu, 2020, Mumunar gobara ya auku a hedkwatar hukumar ayyukan aika da karban sako watau NIPOST dake birnin tarayya Abuja.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng