Jirgin Soji ya ragargaji yan Boko Haram a Sambisa (Bidiyo)

Jirgin Soji ya ragargaji yan Boko Haram a Sambisa (Bidiyo)

- Dakarun Sojin Najeriya sun sake samun nasara kan yan ta'addan Boko Haram

- Jirgin Sojin saman rundunar Operation Lafiya Dole ya lalata mabuyar yan ta'addan dake dajin Sambisa

- Hedkwatar tsaro ta saki faifan bidiyon yadda hukumar Soji ta kai hari da safiyar Juma'a

Yaki da ta'addanci a ranar Alhamis, 2 ga Yuli, ya samu gagarumin nasara yayinda rundunar Operation Lafiya Dole sun ragargaza mabuyar yan ta'addan Boko Haram a jihar Borno.

A bidiyon da hedkwatar tsaro DHQ ta saki a shafin Tuwita ranar Juma'a, 3 ga Yuli, an yiwa yan ta'addan ruwan annaru ne a mabuyarsu dake Mainyakare, cikin dajin Sambisa.

A harin, an kona gidajensu kuma yan Boko Haram da dama sun rasa rayukansu.

Jawabin yace: "Dakarun mayakan saman rundunar Operation Lafiya Dole sun ragargaza wurin ganawar yan ta'addan Boko Haram, gidajensu da kuma hallaka mayakan a Mainyakare, a cikin dajin Sambisa dake jihar Borno."

"An kai wannan harin sama ne jiya, 2 ga Yuli, 2020."

"Jirgin farko ya jefa Bam dai-dai inda ake bukata kuma ya ragargaza shi. Daga baya sauran jiragen suka babbaka sauran gine-ginen da aka nufi kai hari. An kashe yan ta'addan Boko Haram sakamakon hakan."

Kalli bidiyon:

KU KARANTA: Babu rikici ko baraka a APC - Tinubu bayan karban bakuncin shugabannin kwamitin rikon kwarya

A wani labarin daban, Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya shirya taron addu'a na musamman kan harkokin yan bindigan garkuwa da mutane da satar shanu da ya addabi al'ummar jihar shekarun nan.

A ranar Alhamis, 2 ga Yuli aka kaddamar da wannan taron addu'ar kuma za'a kwashe kwanaki uku ana yi, Channels TV ta samu labari.

An fara na yau ne misalin karfe 10 na safe a Masallacin Juma'ar dake birnin jihar inda mahaddata Al-Kur'ani sama da 300 suke sauka.

An kwashe awanni uku a saukar yau.

A cewar masu ruwa da tsaki, an kaddamar da taron addu'ar ne bisa bukatar al'ummar jihar domin shawo kan lamarin rashin tsaron da ya addabi jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel