NCDC: Matasa ‘Yan shekara 20-40 su ke yawo da cutar COVD-19 a Najeriya

NCDC: Matasa ‘Yan shekara 20-40 su ke yawo da cutar COVD-19 a Najeriya

Darekta janar na hukumar NCDC na kasa, Dr. Chikwe Ihekweazu, ya ce matasa masu shekaru 20 zuwa 40 ne su ke taimakawa wajen yada kwayar cutar COVID-19 a Najeriya.

Da ya ke magana da ‘yan jarida domin bayyana inda kwamitin yaki da COVID-19 a Najeriya watau PTF ta kwana, Dr. Chikwe Ihekweazu, ya ce masu matsakaitan shekaru ne su ke yawo da cutar.

Chikwe Ihekweazu ya kuma bayyana cewa manyan mutane da su ka haura shekaru 50 ne su ka fi mutuwa daga cutar Coronavirus mai kawo sarkafewar numfashi.

Zuwa yau Juma’a da mu ke hada wannan rahoto, akwai mutane fiye da 27, 000 da su ka kamu da cutar a Najeriya. Bayan haka akalla mutane 603 ne su ka mutu a sanadiyyar COVID-19.

“Yayin da mutane su ke cigaba da kamuwa da cutar a fadin Duniya kamar yadda babu mamaki ku ke gani. Ya na kara fitowa karara cewa cutar ta fi yawo a cikin yara; matasa masu shekara 20 zuwa 40, ba kananan yara ba.”

Dr. Ihekweazu ya cigaba: “Kuma su na zagayawa da wannan kwayar cuta. Amma a karshe wadanda su ke mutuwa a sanadiyyar cutar, manyan mutane ne wadanda su ka zarce shekara 50.”

KU KARANTA: COVID-19: Babu abin da ya shigo hannun Akwa-Ibom daga gwamnatin tarayya

NCDC: Matasa ‘Yan shekara 20-40 su ke yawo da cutar COVD-19 a Najeriya
Shugaban NCDC na kasa, Chikwe Ihekweazu
Asali: Twitter

Shugaban na hukuamr NCDC mai takaita yaduwar cututtuka a kasa ya ke cewa: “Mutum uku cikin biyar da COVID-19 ta kashe, mutane wadanda su ka haura shekaru 50 ne.”

“Saboda haka, dole mu kara kokari gaba dayanmu wajen kare lafiyar dattawanmu.” Inji Ihekweazu.

Ihekweazu ya ja-kunnen ‘yan Najeriya da su guji tafiyar da ba ta zama dole ba zuwa cikin wasu jihohin. Hakan zai taimaka wajen rage yaduwar wannan cuta a Najeriya.

Da ya ke jawabi, Ministan lafiya, Dr. Osagie Enahire ya ce kawo yanzu an yi wa mutane 138,462 gwajin kwayar cutar. An kuma gano cewa 70% na wadanda cutar ta kama maza ne.

Abin da wannan ya ke nufi shi ne cutar ta kashe tsofaffi fiye da 360 a kasar nan. Haka kuma kusan mutane 19, 000 da su ka harbu da cutar maza ne, ragowar ne kurum mata.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel