Babu rikici ko baraka a APC - Tinubu bayan karban bakuncin shugabannin kwamitin rikon kwarya

Babu rikici ko baraka a APC - Tinubu bayan karban bakuncin shugabannin kwamitin rikon kwarya

- Jagoran APC, Bola Tinubu ya ce babu bukatar sulhu a jam'iyyar

- Ya ce Siyasa ba za tayi dadi ba idan ba'a samun banbancin ra'ayi

- Kwamitin rikon kwaryar APC ta fara aikinta na dinke barakar da ya kunno kai cikin jam'iyyar

Babban jagoran jam'iyyar All Progressives Congress APC, Asiwaju Bola Tinubu, a daren alhamis ya ce babu wata barakar da ake bukatar dinkewa a cikin jam'iyyar.

Sanata Tinubu yace: "Babu rikici a cikin jam'iyyar, babu fada saboda haka babu bukatan sulhu."

Ya bayyana hakan ne bayan ganawar sirri da yayi da gwamnan jihar Yobe, Mai Mala buni, wanda shine shugaban kwamitin rikon kwaryar jam'iyyar a gidansa dake Bourdillon, unguwar Ikoyi na jihar Legas.

Mai Mala Buni ya jagoranci sauran shugabannin kwamitin zuwa Legas don ganawa da Tinubu.

Tinubu yace: "Akwai lokutan da ake samun sabani,hakan ba ya nufin cewa ba zaku iya tattaunawa kan lamarin ba kuma a zama abin koyi a siyasa da shugabanci."

"Amma tambayar a nan itace, shin a shirye muke gaba daya mu gina wannan jam'iyyar da Najeriya? Wannan shine lamarin."

Tsohon gwamnan jihar Legas ya kara da cewa siyasa da babu yan kananan rikice-rikice ba zata yi dadi ba.

Ya ce jigogin jam'iyyar sun amince da shugaban kwamitin rikon kwaryar kuma zasu goya masa baya domin ya samu nasara saboda jam'iyyar ta cigaba da ciyar da kasar gaba.

Babu rikici ko baraka a APC - Tinubu bayan karban bakuncin shugabannin kwamitin rikon kwarya
Babu rikici ko baraka a APC - Tinubu bayan karban bakuncin shugabannin kwamitin rikon kwarya
Asali: Twitter

KU KARANTA: Gwamnatin Neja ta bada N86m don killace Almajirai da mayar da su jihohinsu na asali

Shugaban kwamiti, Mai Mala, ya ce sun kaiwa Tinubu ziyara ne cikin yawon tattaunawa da sukeyi da manyan jam'iyyar.

"Kun san aikin da ke gabanmu na da wuya, kuma muna bukatar shiriya, kwarewa da addu'o'in shugabanninmu." Buni Yace

Gwamnan jihar Legas wanda ya karbi bakuncinsu ya bayyana farin cikin ganin takwarorinsa a jihar.

Yace: "Mun yi tattaunawa mai dadi a ganawarmu na yamman nan,"

Sauran mambobin da suka halarci zaman sun hada da shugaban kungiyar gwamnonin jam'iyyar APC, Gwaman Abubakar Atiku Bagudu; Sakataren kwamitin rikon kwarya, James Akpan Udohehe; da gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel