Gwamnatin Neja ta bada N86m don killace Almajirai da mayar da su jihohinsu na asali

Gwamnatin Neja ta bada N86m don killace Almajirai da mayar da su jihohinsu na asali

A ranar Alhamis, 2 ga watan Yuli, Gwamnatin jihar Neja ta amince da kashe N86 miliyan domin killace Almajirai, ciyar da su da kuma mayar da su jihohinsu na asali, Premium Times ta ruwaito.

Kwamishanar Ilimin jihar, Hannatu Salihu, ta bayyana hakan a hira da manema labarai a Minna, babbar birnin jihar.

Hannatu Salihu ta ce an yi hakan ne bisa shawarar da kungiyar gwamnonin Arewa ta yanke na mayar da Almajirai jihohinsu na asali domin takaita yaduwar cutar Coronavirus.

Ta ce a karon farko, an mayar da Almajirai 86 jihohinsu kuma an hadasu da iyayensu.

Kwamishanar tace a karo na biyu, an mayar da Almajirai 557 cikin 708 garuruwansu na asali.

Ta ce akwai yan kasashen ketare 12 kuma akwai biyu da ba'a gano jiharsu ta asali ba.

A kan lamarin bude makarantu, kwamishanar ya ce ma'aikatar ta zauna da masu ruwa da tsaki har sau biyu domin duba lamarin.

Gwamnatin Neja ta bada N86m don killace Almajirai da mayar da su jihohinsu na asali
Gwamnatin Neja
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Gwamna Aminu Masari ya shirya taron addu'a na musamman kan yan bindigan da suka addabi jihar (Hotuna)

A wani labarin mai alaka, Gwamnatin Jihar Kano ta ce a kalla almajirai guda 193 ne suka kamu da cutar COVID-19 da aka fi sani da coronavirus a jihar.

Kwamishinan Ilimi na Jihar, Sanusi Muhammad Kiru, yayin jawabin da ya yi wa manema labarai a ranar Alhamis ya ce kawo yanzu Kano ta mayar da almajirai 1,500 zuwa jihohinsu na asali.

Ya kuma ce an dawo wa jihar Kano almajirai 4,000.

Har wa yau, ya ce jihar ta haramta makarantun allo, ya ce duk wanda ke son kafa makarantar allo sai ya samar wa daliban dakin kwana.

"Ba za mu amince da yadda Alaramomi ku kwaso dalibai kimanin dubu daya ba amma ba su da wurin da za su ajiye su," in ji shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel