Sabbin mutum 626 sun kamu da cutar korona a Najeriya

Sabbin mutum 626 sun kamu da cutar korona a Najeriya

Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa a Kasa (NCDC) ta ce annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 626 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NCDC ta fitar da misalin karfe 11.43 na daren ranar Alhami 2 ga Yulin shekarar 2020.

A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa karin sabbin mutum 626 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka;

Sabbin mutum 626 sun kamu da cutar korona a Najeriya
Sabbin mutum 626 sun kamu da cutar korona a Najeriya
Asali: Twitter

Lagos-193

FCT-85

Oyo-41

Edo-38

Kwara-34

Abia-31

Ogun-29

Ondo-28

KU KARANATA: Iko sai Allah: An haifa jinjira babu hannuwa da kafafu (Hotuna)

Rivers-26

Osun-21

Akwa Ibom-18

Delta-18

Enugu-15

Kaduna-13

Plateau-11

Borno-8

Bauchi-7

Adamawa-5

Gombe-4

Sokoto-1

Alkalluman da hukumar ta dakile cututtukan ta fitar a ranar Alhamis 2 ga Yulin shekarar 2020 ya nuna cewa jimillar wadanda suka kamu da cutar ta korona a kasar 27,110.

An sallami mutum 10,801 bayan an tabbatar da sun warke sarai, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 616.

A wani labarin daban, Legit.ng ta kawo muku cewa kwayoyin cutar coronavirus sun harbi matar gwamnan jihar Ondo, Misis Betty Akeredolu.

Hakan yana kunshe ne cikin tabbataccen rahoto da wani jami'in gwamnati a jihar ya tseguntawa manema labarai na jaridar Tribune a ranar Alhamis, 2 ga watan Yuli.

Jami'in gwamnatin ya bayyana cewa, "kwanaki biyu da suka gabata ne aka dauki samfurin Uwargidan gwamnan da kuma daya daga cikin dogarawansa, kuma sakamakon da ya fito sa safiyar yau ya tabbatar da cewa suna dauke da kwayoyin cutar."

Sai dai ya bayyana cewa, "tuni uwargidan gwamnan ta killace kanta."

Ya kuma ce "a halin yanzu ana ci gaba da kirdadon sakamakon wasu daga cikin hadiman sadarwa na gwamna da wasu kwamishinoni da ke hulɗa da gwamnan jihar a kai a kai."

Ya ce, a baya bayan nan an gudanar da makamancin wannan gwaji kan 'yan majalisar dokokin jihar da kuma wasu sarakunan gargajiya wadanda suka shimfida goyon bayan kudirinRotimi Akeredolu na neman wa'adi na biyu.

Legit.ng ta ruwaito cewa, ajali ya katse hanzarin kwamishinan lafiya na jihar Ondo, Dr Wahab Adegbenro.

Rahotanni daga fadar gwamnatin jihar sun nuna cewa kwamishanan ya yi gamo da ajali ne sakamakon cutar korona.

Mutuwar kwamishanan ya biyo bayan kamuwar gwamnan jihar da cutar ta Korona.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel