Kwamitin riko na APC ya ziyarci Tinubu a gidansa (Bidiyo)

Kwamitin riko na APC ya ziyarci Tinubu a gidansa (Bidiyo)

Mambobin Kwamitin Rikon Kwarya na Jamiyyar All Progressives Congress (APC) sun yi wata ganawar sirri da jagorar jami'yyar, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a gidansa da ke Bourdillon a Ikoyi a Legas.

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni da Shugaban Kungiyar Gwamnonin Jami'yyar APC, Gwamna Abubakar Atiku Bagudu ne suka jagoranci tawagar.

Kwamitin riko na APC ya ziyarci Tinubu a gidansa (Bidiyo)
Kwamitin riko na APC ya ziyarci Tinubu a gidansa (Bidiyo). Hoto daga Daily Trust
Asali: UGC

Sauran yan kwamitin da suka shiga taron sun hada da Sakataren Kwamitinrikon na APC, Sanata Akpan Udo-Edehe da Gwamnan jihar Legas Gwamna Babajide Sanwo-olu.

A baya, kun ji cewa Kwamitin riƙon APC ta gana da tsohon shugaban wucin gadi na ƙasa na jam'iyyar, Cif Bisi Akande a gidansa da ke Ila Orangun.

KU KARANTA: Iko sai Allah: An haifa jinjira babu hannuwa da kafafu (Hotuna)

Akande, wanda ya shugabanci kwamitin sulhu na kasa na jamiyyar kuma tsohon gwamna ne na jihar Osun.

The Punch ta ruwaito cewa ganawar da su kayi na tsawon awa ɗaya ta mayar da hankali ne a kan aikin da aka bawa kwamitin.

Majiyar Legit.ng ta ce, "Kwamitin ta ziyarce shi ne domin neman shawarwari kan yadda za a sulhunta yan jamiyyar da kara hadin kai.

"Akande na da muhimmanci sosai saboda ya jagoranci kwamitin sulhu da kawo sauyi a jamiyyar da ta karbi korafe korafe fiye da 170.

"Kwamitin ta ziyarci Akande domin samun karin haske akan yadda za ta gudanar da aikin ta na sulhu da hada kan jami'yya."

Shugaban kwamitin rikon, Gwamna Mai Mala Buni ne ya jagoranci mambobin kwamitin zuwa gidan Akande.

Tawagar ta ƙunshi sakataren kwamitin, Sanata Akpan Udoedehe; Gwamnan jihar Osun, Adegboyega Oyetola da Gwamnan jihar Niger, Sani Bello.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel