Buhari ya sake sabunta nadin jakadu 12 - Garba Shehu

Buhari ya sake sabunta nadin jakadu 12 - Garba Shehu

Biyo bayan nadin sabbin kananan jakadu 41, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kuma amince da sabunta nadin wasu tsoffin jakadu 12.

Shugaba Buhari
Hakkin mallakar hoto; Fadar shugaban kasa
Shugaba Buhari Hakkin mallakar hoto; Fadar shugaban kasa
Asali: UGC

Sabunta mukamin nasu ya biyo bayan bita da nazari a kan kwazon aiki da suka yi a baya, wanda bukata ta sanya shugaban kasar ya amince da su ci gaba rike kujerunsu a matsayin jakadu.

Jerin jakadu 12 da kuma jihohinsu wanda aka sabunta nadinsu kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito sun hadar da;

  1. Mrs Uzoma E. Emenike (Abia);
  2. Yusuf M. Tuggar (Bauchi);
  3. Muhammad B. Madugu (Bauchi);
  4. Ambasada Baba Ahmad Jidda (Borno);
  5. Uyigue O. Oghogho (Edo);
  6. Dr Eniola Ajayi (Ekiti);
  7. Deborah S. Iliya (Kaduna);
  8. Mohammed D. Rimi (Katsina);
  9. Farfesa Tijjani Muhammad-Bande (Kebbi);
  10. Dakta Modupe E. Irele (Lagos);
  11. Adeyinka Asekun (Ogun); da
  12. Sanata Goni Modu Zanna Bura (Yobe)

Shugaba Buhari, a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis ta hannun mai magana da yawun sa, Garba Shehu, ya ba ‘yan Najeriya tabbacin yin adalci yayin nadin wakilci da kuma dukkan abin da ya shafi shugabanci.

Shugaban kasar ya ba da tabbacin hakan ne biyo bayan korafin da aka yi kwanan nan bayan nadin sabbin jakadu 41 da ya yi, inda wasu jihohin kasar suka tashi fayau.

Shugaba Buhari, wanda ya sake taya jakadun murna sabunta mukaminsu, ya bukaci da su ci gaba da rike martaba da kuma inganta dabi'un shugabanci a Najeriya, yayin da suke rike kyakkyawar alaka da sauran kasashe.

KARANTA KUMA: Matar Gwamnan Ondo ta kamu da cutar korona

Legit.ng ta ruwaito cewa, a ranar Laraba, 1 ga watan Yuli, shugaba Buhari ya ayyana sunayen mutum 41 da zai nada a matsayin kananan jakadun Najeriya zuwa kashen ketare

Hakan na kunshe ne a wasikar da shugaba Buhari ya aike wa majalisar dattawa na neman amincewarta da mutanen da za su wakilci Najeriya a wasu kasashe na ketare.

Shugaban Majisar Dattawa Sanata Ahmed Lawan, shi ne ya bayyana hakan yayin karanta wasikar a zaman majalisar na ranar Laraba.

Wannan sabuwar bukata da shugaban kasar ya shigar ta biyo bayan amincewar majalisar da sunayen wasu mutum 42 da shugaban ya nada manyan jakadu a watan Mayu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel