Kara farashin man fetur: Babu tausayin jama'a a mulkin APC - PDP

Kara farashin man fetur: Babu tausayin jama'a a mulkin APC - PDP

Jami'yyar Peoples Democratic Party (PDP) ta yi watsi da karin kudin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi daga N123 zuwa N143.80 duk lita.

A cikin sanarwar da sakataren jamiyyar na kasa, Kola Ologbondiyan ya fitar a ranar Laraba ya bayyana karin kudin man a matsayin, "hukunta yan Najeriya ne duba da matsin tattalin arzikin da ake fama da shi a kasar."

"Jami'yyar ta ce babu dalilin yin karin kudin duba da cewa farashin danyen mai ya fadi a kasuwan duniya wadda hakan ya nuna rashin gaskiyar jamiyyar ta APC," in ji Ologbondiyan.

Kara farashin man fetur: Babu tausayin jama'a a mulkin APC - PDP
Kara farashin man fetur: Babu tausayin jama'a a mulkin APC - PDP. Hoto daga The Cable
Asali: UGC

KU KARANTA: Iko sai Allah: An haifa jinjira babu hannuwa da kafafu (Hotuna)

Ya kara da cewa, "Karin kudin man fetur da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta bayar da umurnin yi a lokacin da yan Najeriya ke fama da rashin kudi saboda annobar korona ya nuna rashin tausayawa halin da yan kasar ke ciki."

Jami'yyar ta yi ikirarin cewa matakan da gwamnatin APC ta dauka ya nuna dama ba ta damu da talakawa ba sai dai kara dilmiya su cikin bakar wahala da talauci.

Ta kuma zargi gwamnati mai ci yanzu da bannatar da kudade wurin gudanar da ayyukan gwamnati a kan wasu tsiraru a maimakon yi wa 'yan Najeriya hidima.

A cewar jami'yyar ta PDP, gwamnati mai ci yanzu ta mayar da Najeriya babban birnin talauci na duniya kuma ta kara tabarbara lamarin ta hanyar yin karin kudin man fetur a maimakon nemo hanyoyin magance matsalar.

Ta shawarci fadar shugaban kasa ta rage kudaden da ta ke kashewa wurin tafiyar da gwamnati kana ta kwato Naira triliyan 14 da aka ce an sace a fanin man fetur.

Jami'yyar adawar ta kuma bukaci gwamnati ta janye karin kudin man fetur din da ta yi nan take, ta ce bai dace kudin litar man fetur ya dara N90 ba duba da yadda ake sayar da danyen man a kasuwanin duniya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel