Da karfin iko aka tilastawa 'yan Najeriya yarda da cutar korona - Gwamnan APC
A wani yanayi mai kama da 'dabawa kai wuka', gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya yi zargin cewa 'yan siyasa suna wasa da rayuwar 'yan Najeriya da sunan annobar korona.
Yahaya Bello ya na daga cikin gwamnonin Najeriya biyu da suka musanta cewa an samu bullar annobar korona a jihohinsu - daya gwamnan shine Farfesa Ben Ayade na jihar Kuros Riba.
Shi kansa gwamna Bello an zarge shi da yin wasa da rayuwar mutanen jihar Kogi bayan ya ki amincewa da bullar annobar korona a jiharsa duk da ana zargin ta na cigaba da kashe manyan mutane a jihar.
Amma da ya ke gabatar da jawabi a Lokoja yayin da ya karbi bakuncin kwamitin amintattu na giduniyar Sardauna, Bello ya juya zargin da ake yi ma sa zuwa kan wadanda suka yarda cewa annobar ta harbi 'yan Najeriya fiye da 26,000 tare da kashe mutane 600.
Gwamnan, wanda ya kafe a kan cewa babu cutar korona a jihar Kogi, ya ce cutar ba sabuwa ba ce a Najeriya tare da bayyana cewa akwai hanyoyin da ake maganinta.
Ya ce maimakon a saka dokar kulle da sauran matakan takurawa 'yan kasa, kamata ya yi gwamnati ta mayar da hankali wajen neman hanyoyin magance cutar.
A cewar gwamna Bello, mutuwar alkalin alkalan jihar, Nasir Ajanah, ba ta da alaka da cutar korona, kwanansa ne kwai ya kare.
DUBA WANNAN: Gwamnan Bauchi ya dakatar da shugaban karamar hukuma, mataimakinsa da sakatare
"Ya kamata mu daina wannan wasan, 'yan Najeriya su na shan wahala, sabanin saka dokar kulle da takurawa jama'a, kamata ya yi mu mayar da hankali wajen laluben guraben samar da aiki ga 'yan kasa ta hanyar kera takunkumi tare da fitar da su zuwa kasashen da annobar ta bulla," a cewar Bello.
Sannan ya cigaba da cewa, "korona ba sabuwar cuta ba ce a irin yanayin da mu ke da shi a Najeriya, mu na da hanyoyin maganinta, wajen neman magungunanta ya kamata mu mayar da hankali ba wahalar da jama'a ba da saka mu su dokar kulle ba."
Da ya ke magana a kan mutuwar Ajanah, gwamna Bello ya bayyana cewa; "mun san tarihin larurarsa, dan uwana ne, tun shekarar 2016 mu ke fadi tashin nemar ma sa magani har zuwa wanna lokaci da kwanansa ya kare, bai kamata mu ke wasa da rayukan jama'a ba."
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng