Kwamitin riƙo na APC ta kai wa Akande ziyara a gidansa (Hotuna)

Kwamitin riƙo na APC ta kai wa Akande ziyara a gidansa (Hotuna)

Kwamitin riƙo na jam'iyyar APC jam'iyyar All Progressive Congress, APC, ta gana da tsohon shugaban wucin gadi na ƙasa na jam'iyyar, Cif Bisi Akande a gidansa da ke Ila Orangun.

Akande, wanda ya shugabanci kwamitin sulhu na kasa na jamiyyar kuma tsohon gwamna ne na jihar Osun..

The Punch ta ruwaito cewa ganawar da su kayi na tsawon awa ɗaya ta mayar da hankali ne a kan aikin da aka bawa kwamitin.

Kwamitin riƙo na APC ta kai wa Akande ziyara a gidansa
Kwamitin riƙo na APC ta kai wa Akande ziyara a gidansa. Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

Majiyar Legit.ng ta ce, "Kwamitin ta ziyarce shi ne domin neman shawarwari kan yadda za a sulhunta yan jamiyyar da kara hadin kai.

"Akande na da muhimmanci sosai saboda ya jagoranci kwamitin sulhu da kawo sauyi a jamiyyar da ta karbi korafe korafe fiye da 170.

Kwamitin riƙo na APC ta kai wa Akande ziyara a gidansa
Kwamitin riƙo na APC ta kai wa Akande ziyara a gidansa. Hoto daga The Nation
Asali: UGC

KU KARANATA: Yadda aka gano gawa da kawunan mutum uku a masai

"Kwamitin ta ziyarci Akande domin samun karin haske akan yadda za ta gudanar da aikin ta na sulhu da hada kan jami'yya."

Shugaban kwamitin rikon, Gwamna Mai Mala Buni ne ya jagoranci mambobin kwamitin zuwa gidan Akande.

Tawagar ta ƙunshi sakataren kwamitin, Sanata Akpan Udoedehe; Gwamnan jihar Osun, Adegboyega Oyetola da Gwamnan jihar Niger, Sani Bello.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel