Kogi: Shugaban asusun lamunin tsaro ya rasu

Kogi: Shugaban asusun lamunin tsaro ya rasu

Siaka Oyibo, shugaban asusun lamunin tsaro na jihar Kogi, ya rasu a yau, Alhamis, kamar yadda sanarwar daga gwamnatin jihar Kogi ta bayyana.

Kwamishinan yada labarai da harkokin sadarwa na jihar Kogi, Kingsley Fanwo, ya tabbatar da mutuwar Oyibo a cikin wani jawabi da ya fitar ranar Ahamis.

Oyibi, mai shekaru 69, ya mutu ne bayan ya sha fama da ciwon sukari.

"Honarabul tsohon jami'in rundunar soji ne da ya bawa gwamnatin Yahaya Bello gudunmawa sosai wajen harkar tsaro a matsayinsa na shugaban asusun lamunin tsaro na jiha," a cewar jawabin.

"A yayin da ya mutu bayan ya sha fama da cutar ciwon sukari, za mu cigaba da tuna shi saboda kishinsa, aikinsa tukuru da kuma dagewarsa wajen tabbatar da ganin an kaddamar tsare - tsaren tsaron wannan gwamnati.

"Yau za a binne gawarsa bisa tsarin addinin Musulunci. Ya rasu ya bar iyalinsa. Danginsa da jama'ar karamar hukumar Adavi da jama'ar jihar Kogi za su yi kewarsa.

"Allah ya yafe dukkan kura - kuransa, ya bawa iyali da danginsa hakurin jure rashinsa," kamar yadda ya ke a cikin jawabin.

Kogi: Shugaban asusun lamunin tsaro ya rasu
Marigayi Siaka Oyibo
Asali: Twitter

Duk da hukumar yaki da cututtuka ma su yaduwa (NCDC) ta sanar da cewa an samu mutane uku da suka kamu da cutar korona a Kogi, gwamnatin jihar ta kafe a kan cewa annobar ba ta shiga jihar ba.

DUBA WANNAN: 'Babu batun sulhu': Buratai ya aika sako da babbar murya ga 'yan bindigar Katsina, Sokoto da Zamfara

A ranar Talata ne gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya fito fili ya bayyana cewa an tilastawa 'yan Najeriya yarda da annobar korona ta 'karfin tsiya'.

Ya yi zargin cewa an kirkiri cutar korona ne domin takurawa jama'a da rage mu su tsawon kwanakin da za su yi a duniya.

Kazalika, ya yi kira ga mazauna jihar a kan kar su yarda da bayanan da ake kwafa ana yadawa a kan annobar korona.

Ana zargin cewa annobar korona ta hallaka wasu manyan mutane a jihar Kogi.

A ranar Asabar ne alkalin alkalai na jihar Kogi, Nasir Ajanah, ya mutu a cibiyar killacewa da ke asibitin Gwagwalada a Abuja.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel