'Yan bindiga sun sace mutum 30, sun kashe 'yan sintiri 2 a Nasarawa

'Yan bindiga sun sace mutum 30, sun kashe 'yan sintiri 2 a Nasarawa

'Yan bindiga da adadin su ya kai 50 a ranar Laraba sun sace mutum 30 sun kuma kashe 'yan sintiri biyu a karamar hukumar Nasarawa ta jihar Nasarawa kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban karamar hukumar, Alhaji Muhammad Otto, ya tabbatar da afkuwar hakan inda ya ce, "Yan bindigan sun kashe 'yan kungiyar sintirin biyu a kusa da tsaunin Onda.

"Sun yi wa yan sintirin kwantar bauna ne a yayin da suka bi sahunsu domin ceto mutanen da aka sace.

"An dawo da gawarwakin su zuwa Nasarawa daga tsaunin domin ayi musu jana'iza."

'Yan bindiga sun sace mutum 30, sun kashe 'yan sintiri 2 a Nasarawa
'Yan bindiga sun sace mutum 30, sun kashe 'yan sintiri 2 a Nasarawa. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: UGC

KU KARANTA: Yadda aka gano gawa da kawunan mutum uku a masai

Wata majiyar ta ce wasu yan bindigan da adadin su ya kai 50 sun tare titin zuwa Udege/Loko na tsawon awanni a ranar Litinin.

'Yan bindigan hamsin sun tawo a kan babura ne guda 25 kuma suka sace mutane a daren ranar Litinin.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar, ASP Nansel Ramhan, bai amsa sakon kar ta kwana da wayar da aka masa ba domin jin ta bakinsa game da afkuwar lamarin.

A wani labarin daban, kun ji cewa wata matar aure mai shekara 25 ta datse mazakutar mijin ta a garin Tella da ke karamar hukumar Gassol ne jihar Taraba.

Matar mai suna, Halima ta tafka wannan aika-aikan ne a ranar Talata yayin da mijin ta, Umar Aliyu ke sharbar barci.

Kanin wanda abin ya faru da shi, Shagari Umar, ya ce ihun Aliyu ne ya jawo hankulan mutane inda suka zo suka tarar da shi kwance cikin jini.

Umar ya yi ikirarin cewa, "Mun ga matarsa Halima zaune a gefen gado rike da wukar da ta yi amfani da shi wurin datse mazakutar dan uwanmu."

Ya kara da cewa kiris ya rage fusattaun yan uwan Umar da makwabta suyi mata duka amma, "manya sun shiga tsakani sun ce a tausaya mata saboda tana dauke da juna biyu kuma suka kira 'yan sanda."

A cewarsa, an garzaya da Aliyu zuwa Cibiyar Lafiya ta Tarayya, FMC, da ke Jalingo mai nisar kilomita 150 daga garin Tella.

Ya ce, da isarsu asibitin, an bawa Aliyu kulawa cikin gaggawa aka tsayar da jinin da ke zuba daga raunin bayan an masa tiyata.

Likitan da ya kula da Aliyu, Dr Kyantiki Peter Adamu, ya shaidawa Daily Trust cewa an kira shi sashin wadanda ke bukatar kula cikin gaggawa don wani majinyaci da aka kawo bayan datse masa mazakuta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164