Cutar Coronavirus za ta kara dilmiya talakawa cikin matsanancin talauci - Buhari

Cutar Coronavirus za ta kara dilmiya talakawa cikin matsanancin talauci - Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ana sa ran adadin talakawan Najeriya zai ninku sau uku sakamakon illan da annobar cutar COVID-19 ta yiwa tattalin arzikin kasa.

A takardar da aka saki ranar Laraba, mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya ce Buhari ya bayyana hakan ne a sakon faifan bidiyo da ya aike a taron majalisar dinkin duniya.

A shekarar 2019, rahoton cewa cibiyar lissafi ta kasa NBS ta ce a watan Mayu kadai, adadin yan Najeriya dake rayuwa cikin talauci ya kai 82.9 million.

Shugaban kasa ya ce a fadin duniya, mutane 700, kimanin kashi 10 na adadin al'ummmar duniya na cikin matsanancin talauci.

Buhari yace: "Wadannan mutane kulli yaumin suna fama da rashin ingantaccen abinci, gidajen zama, kiwon lafiya, ilimi da samun ingantaccen ruwan sha.

"A cikin wannan hali, ana sa ran adadin masu fama da bakin talauci zai ninku sau uku saboda dukkan sassan tattalin arziki sun illantu sosai."

Cutar Coronavirus za ta kara dilmiya talakawa cikin matsanancin talauci - Buhari
Buhari
Asali: UGC

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel