Buɗe makarantu: Gwamnati za ta yi ganganci da rayuwar 'ya'yan talakawan Najeriya - ASUU

Buɗe makarantu: Gwamnati za ta yi ganganci da rayuwar 'ya'yan talakawan Najeriya - ASUU

Kungiyar malaman jami'o'i a Najeriya ASUU, ta sake jaddada cewa, akwai bukatar a ci gaba da yin jinkirin buɗe makarantu a fadin tarayyar kasar.

Kungiyar ta ce umarnin da gwamnatin tarayya ta bayar na buɗe makarantu a fadin tarayyar kasar yayin da ake ci gaba da fama da annobar korona, zai iya jefa rayuwar dalibai cikin hatsari musamman talakawan cikinsu.

Shugaban kungiyar ASUU na kasa, Farfesa Bidoun Ogunyemi, sho ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai na gidan Talabijin din Channels a ranar Laraba.

Ogunyemi ya ce, “Abin da muke kokarin yi yanzu shi ne ganganci da rayuwar dalibai. Muna son yin gwaji ne da rayuwar 'ya'yan talakawan Najeriya wajen gano girman tasirin da annobar korona za ta yi."

"Yanzu gwamnati tana nufin a buɗe makarantu ba tare da an yi feshin magani ba a cikinsu? Gwamnatin da za ta iya yin feshin magani a kan hanyoyi da tinuna da kasuwanni."

"Wannan ya nuna cewa ba a dauki rayuwar yaranmu da muhimmanci ba."

"Ya kamata mu yi abin da ya dace, ba wai kawai biyan albashin malamai shi ne kadai da nauyin da rataya a wuyan gwamnati ba. Ya zama wajibi a yi wani yunkuri da zai kawo karshen wannan musiba."

Shugaban ASUU na kasa; Farfesa Biodun Ogunyemi
Hakkin Mallakar Hoto; Jaridar Premium Times
Shugaban ASUU na kasa; Farfesa Biodun Ogunyemi Hakkin Mallakar Hoto; Jaridar Premium Times
Asali: UGC

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, Gwamnatin tarayya ta disashe tunanin bude manyan makarantun gaba da sakandare nan kusa. Ta jaddada cewa babu shirin wannan ci gaban kwata-kwata.

Babban jami'i a kwamitin shugaban kasa mai yaki da cutar korona, Sani Aliyu, shi ne ya sanar da hakan yayin jawabi ga manema labarai a ranar Talata, 30 ga watan Yuni.

KARANTA KUMA: Asarar kudin haraji: Majalisa ta kira Ministar kudi, Emefiele, Magu da wasu kusoshin gwamnati

Matsayar Aliyu ta zo ne bayan gwamnatin tarayya ta ba da umarnin bude makarantu amma ga 'yan ajin karshe a makarantin Firamare da kuma 'yan aji uku da aji shida na makarantun sakandire.

Aliyu ya ce gwamnatin ba za ta yi wani yunkuri da zai zama zagon kasa ga kokarinta ba ta hanyar bude manyan makarantun gaba da sakandire.

Ya kara da cewa dukkan matakan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aminta da su, ya yi hakan ne saboda a rage yawan masu cutar a kasar.

Aliyu ya ce ya zama dole a bude makarantu a yanzu ga 'yan ajin karshe don gudun kada su yi asarar wannan shekarar dukkanta saboda annobar Covid-19.

Ya kara da cewa, gwamnatin tarayya za ta dauki matakai masu tsauri wurin tabbatar da cewa sashen ilimin kasar nan bai yi asarar shekara daya ba cif saboda annobar korona.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel