Har yanzu da sauran rina a kaba - Shugaban WHO yace yayinda adadin masu Korona ya haura miliyan goma

Har yanzu da sauran rina a kaba - Shugaban WHO yace yayinda adadin masu Korona ya haura miliyan goma

Watanni shida da bullar cutar Korona a duniya, sama da mutane miliyan goma sun kamu da cutar kuma akalla 500,000 sun rasa rayukansa, lissafin jami'ar Johns Hopkins ya nuna.

Shugaban kungiyar kiwon lafiyan duniya WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce har yanzu duniya bata ga komai game da cutar ba tukun saboda mutane da yawa zasu sake kamuwa muddin gwamnatoci basu dau matakin kwarai ba.

Tedros Ghebreyesus ya yi bayani ranar Litinin a taron yanar gizo cewa "watanni shida da suka wuce, babu wanda ya taba tunani rayuwarmu zata shiga wani irin hali da wannan cutar ta jefa mu."

"Dukkanmu muna son wannan abun ya kare. Amma maganar gaskiya itace ko kusa da karshe ba'a zo ba."

"Duk da cewa kasashe da dama sun samu wasu nasarori, cutar na kara yaduwa a fadin duniya."

"Muna cikin wannan abin har na lokaci mai tsawo."

"Muna bukatar jajircewa, hakuri, kan-kan da kai, da sadaukarwa a cikin watannin nan na gaba."

Har yanzu da sauran rina a kaba - Shugaban WHO ya ce yayinda adadin masu Korona ya haura milyan goma
Shugaban WHO
Asali: UGC

KU KARANTA: An nada Ganduje shugaban kwamitin yakin zaben gwamnan jihar Edo na APC (Kalli jerin yan kwamitin)

Za ku tuna cewa an tabbatar da bullar cutar Korona da mutane 41 a ranar 10 ga Junairu. A yanzu cutar ta game dukkan nahiyoyin duniya da kasashe sama da 200.

Kawo lokacin da muke wannan rahoto, mutane 10,590,953 sun kamu da cutar a fadin duniya bisa lissafin shafin worldometers.info dake bibiyan wadanda suka kamu da cutar.

Daga cikin kasashen da abin yafi shafa sune Amurka, Brazil, Indiya, Italiya, Faransa da Andalus.

Amma Amurka, Brazil, Rasha da Indiya ne aka fi samu saboda mutane miliyan biyar aka tabbatar sun kamu a kasashen.

A yanzu haka, mutane 4,277,962 ke jinya a asibiti. Daga cikin wannan adadi, 4,220,122 basu cikin mawuyacin hali amma 57,840 na cikin halin mai wuya kuma ana tsoron zasu iya mutuwa.

Amma dai mutane 5,798,970 sun samu waraka a fadin duniya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel