'Yan Najeriya sun yi martani kan karin kudin litar man fetur zuwa N143.8

'Yan Najeriya sun yi martani kan karin kudin litar man fetur zuwa N143.8

'Yan Najeriya, a ranar Laraba sun nuna rashin jin dadinsu game da karin kudin litar man fetur da gwamnatin tarayya ta yi da fiye da N20, inda ta ce ba a wannan lokacin ya dace a yi karin ba.

A halin yanzu ana sayar da litar man fetur daga N140.8 zuwa N143.8 a gidajen man fetur a sassan kasar a maimakon farashin na baya na N121.50 zuwa N123.50.

Karin yana zuwa ne a lokacin da gwamnatin tarayya ke dage dokar hana zirga zirga tsakanin jihohi da ta saka domin dakile yaduwar cutar coronavirus.

Gwamnatin ta yi karin ne sakamakon shawarar da Hukumar Daidaita Farashin Man Fetur na Kasa, (PPPRA) ta bayar a karshen watan Yuni.

'Yan Najeriya sun yi martani kan karin kudin litar man fetur zuwa N143.8
'Yan Najeriya sun yi martani kan karin kudin litar man fetur zuwa N143.8. Hoto daga The Nation
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Mata mai juna biyu ta datse mazakutar mijinta da wuka a Taraba

Duk da cewa gidajen man da Daily Trust ta ziyarta a Legas da Abuja a jiya Laraba ba su canja farashinsu ba tukuna, wasu 'yan Najeriya da dama da suka bayyana ra'ayoyinsu sun ce karin ya zo a lokacin da mutane ke cikin matsi.

Ana daura wa 'yan Najeriya nauyin da ya fi karfinsu – NLC

Hukumar Kwadago ta Kasa, NLC, ta nuna rashin jin dadin ta game da karin kudin man fetur din da ta ce cin zalun mutane ne.

Shugaban NLC, Ayuba Wabba ya shaidawa majiyar Legit.ng a wayar tarho cewa bai kamata a wahalar da 'yan Najeriya ba saboda sakacin gwamnati.

Wabba ya ce, "Wannan zaluncin ba za ta zo karshe ba har sai lokacin da muka fara tace danyen mai da kanmu a Najeriya.

"Mun sha nanata wannan cewa ba mu amince da shi ba, ina ganin a wannan lokacin gwamnati ce ya dace ta bawa mutane ba mutane su bawa gwamnati ba, ana zaluntar mutane ta kowane bangare.

"Za muyi martani a hukumance domin sai yanzu na samu labarin."

Kungiyar masu motoccin haya, (PTONA) ita ma ta bayyana rashin jin dadin ta a kan wannan karin kudin na man fetur.

Sakataren, PTONA, Ebere Oluoha a hirar da ya yi da majiyar Legit.ng ya ce karin kudin man bai yi wa mutane dadi ba.

"Don mene za ka kara kudin man fetur a yanzu? Ba wannan lokacin ya dace ba," in ji shi.

A cewarsa wannan zai saka masu motocci su kara kudin mota a yanzu da ake bude iyakokin jihohi.

Kazalika, wani kwararren mai nazarin magunguna da ke zaune a Abuja, Abubakar Abdullahi, ya ce ya kamata gwamnatin tarayya ta dena yawan canja farashin man fetur.

Abdullahi ya ce yana goyon bayan a sayar wa yan kasuwa matattun mai na kasar "don za su fi basu kulawar da ya kamata.

"A kasashen da suka ci gaba, 'yan kasuwa ke kulawa da muhimman bangarorin samar da ayyukan more rayuwa."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel