Daga karshe: FG ta yi magana a kan bude makarantun gaba da sakandare

Daga karshe: FG ta yi magana a kan bude makarantun gaba da sakandare

- Gwamnatin tarayya tace har yanzu ba a tsara shiri mai kyau ba da zai sa a bude makarantun gaba da sakandare

- Mashiryin PTF, Sani Aliyu, ya bada wannan sanarwar yayin da yake cewa ana kokarin ganin an rage yawan masu kamuwa da cutar

- Aliyu ya ce bude makarantu saboda masu kammalawa a wannan shekarar ya zama dole saboda gudun asararta dukkanta

Gwamnatin tarayya ta disashe tunanin bude manyan makarantun gaba da sakandare nan kusa. Ta jaddada cewa babu shirin wannan ci gaban kwata-kwata.

A yayin jawabi ga manema labarai a ranar Talata, 30 ga watan Yuni, Sani Aliyu ya sanar da hakan a yayin da ake shiga sabon kashi na kulle a kasar nan.

Matsayar Aliyu ta zo ne bayan gwamnatin tarayya ta sanar da bude makarantu amma ga masu kammalawa a wannan shekarar a fadin kasar nan.

Aliyu ya ce gwamnatin ba za ta yi hakuri ko wani yunkuri da zai zama zagon kasa ga kokarinta ba ta hanyar bude manyan makarantun gaba da sakandire.

Ya kara da cewa dukkan matakan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aminta da su, ya yi hakan ne saboda a rage yawan masu cutar a kasar nan.

Daga karshe: FG ta yi magana a kan bude makarantun gaba da sakandare
Daga karshe: FG ta yi magana a kan bude makarantun gaba da sakandare
Asali: Twitter

KU KARANTA: An birne bama-bamai a kananan hukumomi 7 na jihar Yobe (Sunaye) - 'Yan sanda

Aliyu ya ce ya zama dole a bude makarantu don masu kammalawa don gujewa asarar wannan shekarar dukkanta saboda annobar Coronavirus.

Ya kara da cewa, gwamnatin tarayya za ta dauka matakai tsaurara wurin tabbatar da cewa sashen ilimin kasar nan bai yi asarar shekarar daya ba cif saboda annobar korona.

"A takaice, babu wani shiri na bude manyan makarantun gaba da sakandare har sai mun ga yawan masu kamuwa da cutar a kullum suna raguwa," Aliyu yace a wani shirin gidan rediyo.

A ranar Litinin da ta gabata, gwamnatin tarayya ta amince da bude makarantu a fadin kasar nan. Hakan ya biyo bayan taron da ya wakana tsakanin kwamitin yaki da cutar korona na fadar shugaban kasa da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Kamar yadda gwamnatin tarayyar ta bayyana, azuzuwab da za su koma bakin karatun sun hada da:

1. Aji shida na dukkan makarantun firamare.

2. Daliban aji uku da na aji shida na makarantun sakandaren da ke fadin kasar nan.

Hakazalika, gwamnatin tarayyar ta amince da bude shige da fice tsakanin jihohin kasar nan, amma matukar ba a zarta lokutan doka ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel