Shugaba Buhari ya hana alfarma wurin daukan aiki a Najeriya - Lai Mohammed

Shugaba Buhari ya hana alfarma wurin daukan aiki a Najeriya - Lai Mohammed

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake gargadin ma’aikatu, cibiyoyi da hukumomin gwamnati, a kan yiwa masu rike da mukaman siyasa da sauran jami'an gwamnati alfarma wajen daukan aiki.

Shugaban kasar ya ce alfarmar da ake yiwa masu rike da mukaman siyasa da sauran manyan jami'an gwamnati sakamakon matsayinsu wajen nemo aiki ga wadanda suke so ta haramta.

Wannan gargadi na shugaban kasar yana kunshe ne cikin wata sanarwa da minista labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed ya fitar cikin birnin Abuja a ranar Laraba.

Kamar yadda sashen Hausa na BBC ya ruwaito, shugaban kasar ya ce wannan mummunar dabi'a ta saba wa dokar gudanarwa ta aikin gwamnati da kuma hukumar tabbatar da ɗa'ar ma'aikata.

Shugaban Najeriya; Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya; Muhammadu Buhari
Asali: UGC

Ministan ya ce gargadin shugaban kasar ya biyo bayan korafe-korafen da ake yi na cewa wasu manyan jami'an gwamnati da masu rike da madafan iko na amfani da matsayinsu wajen neman aiki da kuma kwangiloli.

Alhaji Mohammed ya ce shugaban kasar ya kuma gargadi wadanda aka yi nadi na siyasa da sauyan kusoshin gwamnatin a kan yi amfani da matsayinsu wajen neman alfarma ta dauka aiki alhali ba tare da sun cancanta ba.

Ministan ya ce hukumomi da ma'aikatu su yi fatali da duk wasu bukatu da wani jami'in gwamnati ya turo musu na neman aiki ko kuma kwangila ga wani.

KARANTA KUMA: 2023: Ghali Umar, Shehu Sani, Falana da wasu 'yan gwagwarmaya 27 sun kirkiro wani sabon salo na siyasa

Ya ce wajibi ne gwamnati ta fitar da ka'idodi da tsare-tsaren da suka dace a shimfida a yayin bayar da aiki ko kuma kwangila.

Haka kuma Legit.ng ta ruwaito cewa, hukumar tara haraji ta jihar Kano, KIRS, ta dakatar da wasu ma'aikata 308 daga aiki na wani ɗan lokaci sakamakon raguwar samun kudaden haraji da jihar ta yi.

Shugaban KIRS, Bala Inuwa, shi ne ya sanar da hakan yayin da yake zantawa da manema labarai cikin birnin Kanon Dabo a ranar Laraba.

Wannan lamari kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, ya faru ne a sakamakon durkushewar tattalin arziki da annobar korona ta haddasa.

Ya kuma bayyana cewa an yi watsi da kamfanonin tuntuba guda 60 masu bawa hukumar shawara wadanda kwangilarsu ta kare tun a shekarar 2018 kuma su ke ci gaba da aiki ba bisa ka'ida ba.

Sai dai ya ce kamfanonin da ke da sha'awar ci gaba da wannan kwangila na iya sake nema da shigar da bukatar hakan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel