Gwamnan Plateau, Simon Lalong, ya shiga killace kansa bayan kwamishanansa ya kamu da cutar Korona

Gwamnan Plateau, Simon Lalong, ya shiga killace kansa bayan kwamishanansa ya kamu da cutar Korona

Gwamnajihar Plateau, Simon Bako Lalong, da wasu mambobin majalisar zartarwas sa sun shiga killace kansu bayan kwamishanan masana'atu da kasuwanci, Abe Aku, ya kamu da cutar Coronavirus.

Kwamishanan labaran jihar, Dan Manjang, ya bayyana hakan ne a takardar da ya saki ranar Laraba.

A cewarsa, Lalong ya umurci sukkan kwamishanoninsa su garzaya a yi musu gwajin cutar ta COVID-19.

Manjang yace: " Bisa umurnin gwamna, za'a dauki samfurin kwamishanoni domin kai su dakin gwajin cutar COVID-19 dake National Veterinary Research Institute (NVRI), Vom, domin gwaji."

"Yayinda ake sauraron sakamakon gwajin, ana kira ka al'umma su guji kai ziyara wajen mambobin majalisar zartaswar jihar inda suka killace."

"An dau wannan mataki ne domin takaita yaduwar cutar da kuma nuna cewa shugabanni ke kan gaba wajen bin doka."

KU KARANTA: An damke Fasto mai shekaru 54 ya yiwa 'yar 12 fyade:

Kwamishanan ya kara da cewa gwamna Lalong da iyalansa basu kamu da cutar.

Hakazalika ya yi kira da al'ummar jihar su tabbatar da cewa suna bin ka'idojin hana yaduwar cutar da aka gindaya.

Ya gargadi duk wanda aka kama yana saba dokar zai shiga hannun hukuma zuwa za'a hukuntashi.

Gwamnan Plateau, Simon Lalong, ya shiga killace kansa bayan kwamishanansa ya kamu da cutar Korona
Gwamnan Plateau, Simon Lalong, ya shiga killace kansa bayan kwamishanansa ya kamu da cutar Korona
Asali: Facebook

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel